Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa sunan Taiwo Oyedele domin naɗa shi a matsayin ƙaramin ministan kuɗi.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce an aika sunan Oyedele zuwa Majalisar Dattawa domin tantance shi ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
Oyedele zai maye gurbin Doris Uzoka-Anite.
Ita kuma an mayar da ita Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa a matsayin Ministar Ƙasa.
Wannan shi ne muƙaminta na uku a wannan gwamnati.
Oyedele ƙwararre ne a fannin tattara haraji, kuma masanin tattalin arziƙi da lissafi ne.
Ya taɓa zama shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Tsarin Haraji.
Ya yi aiki na shekaru da dama a kamfanin Price water house Coopers (PwC), inda ya kasance jagora a harkar haraji a Afirka.
Ya yi karatu a Yaba College of Technology, sannan ya samu digiri daga Oxford Brookes University.
Haka kuma ya halarci manyan shirye-shiryen a Harvard Kennedy School da sauran manyan makarantu.
Oyedele na daga cikin waɗanda suka jagoranci tsara sabbin dokokin haraji a Nijeriya.
An amince da dokokin ne bayan muhawara mai tsawo a Majalisar Tarayya, sannan Shugaba Tinubu ya rattaba musu hannu a watan Yunin 2025.
Dokokin sun fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, 2026.
Ana sa ran naɗinsa zai ƙara ƙarfafa gyaran tsarin haraji da ƙara samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati tare da bunƙasa zuba jari a ƙasar.

Post a Comment