Fitaccen ɗan jarida kuma mai sharhi kan harkokin kafofin watsa labarai, Tucker Carlson, ya ce hukumomin Saudi Arabia da Qatar sun kama wasu jami’an da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Mossad waɗanda ake zargin suna shirin kai hare-haren bama-bamai a ƙasashen biyu.
Carlson ya bayyana hakan ne a yayin wani shirin sa na baya-bayan nan da aka yaɗa sosai a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, inda ya ce, “A daren jiya, a duka Qatar da Saudi Arabia, hukumomi sun kama jami’an Mossad da ke shirin kai hare-haren bama-bamai.”
Ya kara da cewa wannan ba wani babban barazana ba ce ga ɓangaren Isra’ila a ganinsa. Carlson ya yi zargin cewa manufar shirye-shiryen ita ce lalata zaman lafiyar yankin.
“Sun so su raunana yankin Tekun Fasha, kuma cikin kwanaki biyu sun cimma hakan,” in ji shi. Ya kuma bayyana fatan cewa ƙasashen Tekun Fasha za su dawo da kwanciyar hankali da ci gaba.
Ya jaddada cewa ƙasashen Tekun Fasha abokan hulɗa ne na United States, yana mai kawar da zargin cewa Amurka na da hannu a shirye-shiryen.
“Ƙasashen Tekun Fasha ba barazana ba ne gare mu. Muna da sansanonin soja a waɗannan ƙasashe. Waɗannan ƙasashe suna cikin manyan abokan hulɗarmu, har ma sun fi kusa da mu fiye da Isra’ila,” in ji shi.
Ya ce ƙasashen yankin abokai ne, amma sun sha wahala sosai, musamman ya yi magana kan Dubai.
Ya bayyana cewa kai hare-hare kan Dubai na iya yin illa ga tattalin arzikinta da kuma kuɗaɗen da take samu daga yawon buɗe ido.
“Filin jirgin sama na Dubai na ɗaya daga cikin mafi cunkoson filayen jirgin sama a duniya. Idan mutane suka fara ganin hotunan hayaki a filin jirgin saman Dubai a shafukan sada zumunta, mutane za su fara tunanin canza wurin hutawa,” in ji shi.
Ya ce irin waɗannan hare-hare na iya yi wa ƙasashen yankin illa sosai ta fuskar tattalin arziki da yawon buɗe ido.
Carlson ya zargi gwamnatin Israel da neman haifar da rikici a ƙasashen yankin, yana cewa manufar ita ce raunana Iran da Qatar da UAE da Saudi Arabia da Bahrain da Oman da Kuwait.
Rahoton ya bayyana cewa waɗannan kalamai sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da wani sabon farmakin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran, wanda ake zargin ya haɗa da kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula da na tsaro a ƙasar.

Post a Comment