Sabon Salon Mamayar Afrika A Karo Na Biyu –Shaikh Zakzaky

 


Wannan wani ɓangare ne daga ƙarshen jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda ya gabatar ga dandazon dubban ’yan’uwa da suka halarci taron Yaumush Shuhada, a ranar Asabar, 25 ga watan Rajab, 1435H (24/5/2014), a filin Polo da ke kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, a garin Zariya. Dandalin Yaɗa Labarai (Media Forum) na Harkar Musulunci ne ya rubuta wannan domin amfanin masu karatu.

A cikin jawabin, Sheikh ɗin ya yi bayani kan makirce-makircen da ke tattare da hare-haren da ake kai wa wasu yankuna, kamar kauyukan Zamfara, Birnin Gwari da makamantansu, tare da bayyana cewa waɗannan hare-hare wani ɓangare ne na shirin sake mamayar Afirka ta hanyar amfani da abin da ake kira “ta’addanci”, a karo na biyu.

MAMAYAR AFRIKA

Kunga yanzu muna fuskantar wani abu a kasarnan. Dama can na sha wannan maganar cewa; akwai wani abu yana nan tafe.  A wa’azuzuka daban-daban na ambata wannan. To, Akwai wani abu na tafe, shi ne; mamayar Afrika. Wanda suka ce, sun yi nazari sunga cewa; karnin da za a shiga (tun kafin ma a shiga), tun kafin a shiga karnin nan. 2000 din nan. Tun a 1900 suke fada. Suka ce; karni na gaba, sunansa KARNIN AFRIKA. Domin sun yi nazari sun ga cewa, Afrika na da kusan kashi biyu bisa uku na dukkan dukiyan da ake da shi a duniya. Saboda haka za a sake kama Afrika na biyu. Sabon rububi. Abin da aka kira ‘scramble for Africa’. Suka ce za a yi ‘second scramble’.

Za a yi sabon rububi. Saboda lokacin rububin Afrika na wancan karon. Tsakanin daulolin Turai da Ingila da Faransa da ‘Germany’ da ‘Italia’ da ‘Portugal’ da ‘Belgium’, duk kowanne, wannan ya kama nan, wannan ya kama nan, wannan ya kama…. Har suka je ‘Berlin, suka yi ‘conference’ aka raba. Kowa ya fadi inda ya kama aka tsaga aka ba, aka ce; kowa ga nasa. To, sunce za a yi wannan karon.

To, sai kuma Amerika ta zo ta ambata ta ce; zata yi amfani da ta’addanci wajen sake kama Afrika. To, shiyasa ku ga wannan abin da yake faruwan yanzu. Sun yi a Libya. Bayan lokacin da suka ji dagowar Larabawa din nan, da dagowar Misra, abin ya firgita su, suka ce, to, suma bari su yi na su. Sai suka yi a Libya. Suka je suka rugurguza Libya din, suka kashe Gaddafi. Yanzu ba komai dake gudana a Libya banda kashe-kashe da fada na Kabilanci. Tsakanin Melisha da kabila. Da na warin launi. Su ko suna diban dukiya.

To, dama da Libya da Nijeriya ance su suke da mai din da ake ce mishi; mai zaki – ‘sweet crude’. To, na Libya yanzu dama na su ne. Na Nijeriya dama na su ne. Tunda suna samun gaulaye ne su ajiye. Kullum ba su da wani aiki, sai dai su samo wani Gaula su ce shi ne shugaban kasa, su samo Dolo su ce shi ne mataimakinsa, su sami Gabo su ce shi ne Gwamna, su samu Wofi su ce shi ne Minista, su sami, ga sunan. Su yi ta tatsan arziki din.

SALON MAMAYAN KASA

To, yanzu kuma sai suka zo da wani salon, to, mamayan kasa. Saboda haka suka shirya suka mamaye Mali. Yanzu ko shekaran jiyan nan a labaru suna cewa; an fafata a Kidal da Gawo da wa’insu ‘yan bindiga. Haka kawai za su bayyana a unguwa su yi ta zubar da wuta, bakasan wa ake harbi ba. A ce ai wasu ne masu kishin Islama ne suka bayyana ana fafatawa. Alhali Mali, Zinariya suka gano a Mali. Zinariyar da ba a san inda take ba tuntuni. Don dama ana da labarin akwai Zinare a Mali. Mansa Musan nan, wanda ya yi tafiya zuwa Hajji. Wanda ya shiga tarihi. Wanda aka ce, ya tafi da Rakuma dubu dauke da kayan Zinare da Bayi dubu, kowanne yana dauke da Sandan Zinare.

Da yaje Misra, Zinaren da ya kai Misra sai da ya sauke farashin Zinare da har yanzu bai tashi ba. Da yaje Makkah ya yi gine-ginen da sai kwanannan ne Ali Saud suka rusa wasu. Suka rurrusa suna gine-ginen su a gewayen harami. Amma har ya zuwa dan shekarun baya gine ginen Mansa Musa abin kallo ne. To, Gwal din nan ba a san inda yake ba. An san akwai Gwal. A ina ne ma Mansa Musa ya yi fada, ba a sani ba. Ko su ce, NAWA ne, ko su ce Iraira, ko su ce kaza ne, Bil ne, a je Bil a shafa ba a gani ba. A ce wannan garin ne, a je ba za a gani ba. To, yanzu sun gano Gwal din, saboda haka, suka tsara yadda suka mamaye Mali. Suka ce ‘yan kishin Musulunci ne suka fada daga Aljeriya. Ba dan Mali ko daya a cikinsu. Wai sun kama rabin Mali fiye ma da rabi, sun kafa daula wai sunanta ‘Azwat’.

Sannan sai Faransa maza wuf ta shiga wai ta fatattake su. Ta riga Amerika shiga. Don Amerika ita ta shirya shiga. Sai suka (Faransa suka yi wuf)… wai sun fatattake su. Bayan wannan, sai Faransa, akwai ‘Diamond’ a Central Africa, shi ne; sun je diban ‘Diamond’ ne sai suka hada fada. Wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba.

Wai su Saleka, suka shiga cikin Central Africa Republic, suka yi ta kashe Kiristoci suna kona Cocina da sunan wai su Musulmi ne. Sannan su ba ‘yan Central Africa Republic. Suka fita kasar. Bayan sun fita Afrika ta tsakiya, sannan sai suka kawwana Melisha na kirista wai su ‘Anti Balaka’. Sai suka bi suna kashe musulmin da suke zaune a kasar. Wai suna ramuwar gayya. To, imma wa’incan Saleka sun zo sun kashe ku, ‘yan kasar ku ne? Daga wani wuri fa suka shigo, suka kuma fita. Waima su suka fara.

Kamar yadda suka yi juyin mulki a Mali. Suka wani wai shi Sanogo ya zama shugaba. Wai shi ya yi juyin mulkin akan cewa, shi Sulaimanu Traore ya kasa ima ‘yan tawayen Arewa. Sai kuma aka ce, ‘yan tawayen Arewa din ma sun kwace kasar gaba daya ma a karkashin shi Sanogo din.

To, nan ma na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, sai aka ce, wai wani musulmi ya yi juyin mulki na soja. Wai sunanshi Michael Odofia. Kun taba jin sunan musulmi Michael? Wai Musulmi ne, amma sunanshi Michel Am-Nondokro Djotodia. Wai Djotodia Michel ya kwace mulki. Wai shi musulmi ne. Ya za a yi Musulmi ya zama shugaban kasar a inda mafi Yawa Kirista ne? Ashe haramun ne Kirista ya zama shugaban Kasa a kasan da yake mafi yawan su Musulmi ne, shi ne har aka samu Kiristoci suka zama shuwagabanni a Nijeriya?

Da wannan suka fake, suka je suka shiga cikin Central Africa suna ta kashe Musulmi musamman Fulani makiyaya wanda ba-su-ji-ba-ba-su-gani ba. Diamond suka je diba. Kudancin Sudan da suka ga ba zai yiwu sukai cewa; ‘yan kishin Isalama ba ne, sai suka hada fadan Kabila tsakanin Dinka da Nod. Amma shi ne, hana ma China Mai. Ya zama tunda dama Kudancin Sudan suna dasawa da China, ya zama ba su tare da China.

Nijeriya kuwa, shi ne suka bullo da wani abu wai shi Boko haram. Wanda tuntuni su wasu ba’adin Amurkawa sun riga sun ambata sanannen abu ne cewa, ba wani abu wai shi Boko haram, kikkiran Amerika ne.  To, yanzu gashi wai Boko haram sun sace wasu ‘yan mata a wata Makaranta, amma su ‘yan matan da iyayensu sun san suwa suka sace su. Sun sani sarai, gwamnatin Jonathan ce. An ce ana ta zanga-zanga, na ce; wai ana zanga-zangar me ne? Harda jan kaya. Ina jan kayan ya fito? Wai ku bamu ‘yan matanmu. Wa zai baku? Jonathan ko Shekau? Idan Jonathan ne zai baku ‘yan matan ku, eh, to, ku yi mishi zanga-zanga ya fito da ‘yan matan inda yasan ya ajiye. Don yasan Barikin Sojan da ya ajiye su. Idan ko Shekau ne, kunsan a wacce Sheka yake? Yaushe yake jin ku? Yana nan shima suna tsare da shi a wani Barikin Soja. Don kayan su ne duka.

BOKO HARAM SUN SHIGO NA SOSAI, SU NE AMERIKA

Ba wata tsiya wai ita Boko Haram, karyar tsiya ce kawai. Wannan iskancin din bamu za a yi wa ba. Idan kuna so ku zo ku diba Mai ku diba, zinariya ku diba arziki, ku zo a yi ciniki. Ko da cinikin ‘Mugabala’ ne. Mu ba ku Kwai ku bamu Kaza. Ko, mu baku Rakumi ku bamu Rago. Mun yadda gwara haka nan. Amma kwazo ku yi mana iskanci da addininmu. Ku ce mana muna fama da musulmi masu kishin addini kun zo ku cece mu. Alhali mun san kun zo ku cuce mu ne.

To, ga Boko haram din sun shigo na sosai, su ne; Amerika. Suna shigowa ko, yalai sai kashe-kashe. Sai tashe-tashen bama-bamai. To, kuma wannan irin shi fa suka yi a Afghanistan ko kuma suke yi har yanzu. Kuma irin shi suke yi har yanzu a Irak. A Afghanistan suna da filaye gomomi ne na filayen jirgin sama suna kwasar dukiyoyi. Da sunan suna yaki ne. Asali sun shiga da cewa; suna neman Bin Laden ne. Ba a san inda Bin Laden yake ba. Can kuma suka ce; Bin Laden din ma sun kashe shi a wani wuri ma ba a Afghanistan din ba.

To, suna mene ne a Afghanistan? Har yanzu suna nan. Irak ko suka shiga suka ce akwai WMD. Suka rugurguza Irak. Suna ta cewa; za a ga WMD din. Za a gani. Can sai kuma, har suka kamo Saddam ma, har cocila suka kunna suna kallon bakinsa, imma WMD din yana cikin bakin Saddam ne, duk sun dudduba. Sai suka juya kuma wai suna kai musu Dimokuradiya ne. Yanzu kuma sun ce ba WMD amma ba su bar Irak ba. Suna nan suna tatsar dukiya. Kullum sai tashe-tashen bama-bamai da kashe-kashe. Kuma su suke yi.

To, yanzu tunda suka shigo nan muma abin da suka yi mana shiri ke nan. Haka kawai mun yi gari abin da muke jin labari a wasu kasashe ya kunno mana bagtatan. Mun tabbatar ba wata kungiya wai ta kishin Islama wai wanda ake ce ma ta wai Boko Haram. Mun tabbatar ba ta. Ba ta da wujubi sam-sam. A ina? A wani gari? A wani titi? A wacce unguwa?

Amma bama-bamai na tashi. Su suke sa bam-baman nan. Ko su haka rami wawukeke su saka su birne ko su matsa ‘remote’ ko su zo da mota su ajiye su danna. Aikin ke nan. Ko wasu su bayyana su bude wuta. Saboda mene? Dukiya suka zo di ba.

DUKIYAR MU SUKA ZO ƊIBA

A tsakanin Zamfara zinare ke kwance, suna so su share Eriyan da Zinare yake ne, ya zama ba mutum ko kadan, su yi filin jirgin sama, su yi sansanin Soja su rika kwasan Zinariya. Nan tsakanin Zariya da Birnin Gwari, Zinare ne yake kwance da duwatsu masu daraja. So, suke su share mutanen wurin su kafa filin jirgin sama su kwasa. Tsakanin Sakwkwato har zuwa Borno, daga Uranium sai Zinare sai Platinum. Shi suka zo ɗiba. To, ku zo mana ai ciniki. Ko da ma ku bamu Kaza mu baku Rakumi, amma ku barmu da ranmu kuma ku kyale mana addininmu.

Amma mene ne na cewa; zaku shigo ne, da yinma mutane wayayyu babarodo. Ina ku kuke da wayon? Yaushe aka yi Ba’amurke? Yaushe aka yi Bature ma tukunna? Wani wayo yake da shi? Eh mana. Dauko tarihin Bature ka karanta mana, bagidaje, maye, ɗan bori! Yaushe ya waye harda zai mana wayo? Rashin kunyan banza kawai. Ku zo ai ciniki. Kuna da Bindiga mun sani, kun iya kisan kai, amma a kyale mana addininmu.

To, yanzu abin da ya kawo su ke nan kuma yanzun musiban yana rutsawa nan da nan tsakanin ‘yan’uwa. Kun san a Gwoza. Harma sun rutsa da garin Gwoza, sun ce, ba za su shiga ba, saboda suna jin tsoron ‘yan shi’a. Don akwai wani dan uwa da suka kama suka cire masa kai, suka fille kansa sosai, amma sai suka ji kalma, kan na Kalmar shahada. Suka duba ga Kai yana ‘la’ilaha illallah Muhammadur Rasulillah’ ga gangan jiki din. To, shi ne suka ce; suna jin tsoron garin saboda ‘yan shi’a. To, wannan abin da muke fuskanta ke nan. Kuma na san sun riga sun ambata tuntuni, abin da suke jin tsoro kawai ita ce; wannan Harka din. Don sun san ita ce kawai za ta taka musu burki.

KIRA GA SU WADANNAN MUTANEN

Amma muna ma kira ga su wa’innan mutanen, mun ji an kira ka baka ci zabe ba ance kaine kake da mukami, mun ji baka cancanta ba, mun ji kai Gaula ne, ko Gabo ne ko Sakarai ne ko Shashasha ne, ko Wofi ne, to, mun ji kaine. Yanzu ko a haka nan ka yadda yanzu a baka kudi a kashe mutanenka? Kai baka da tunani? Shi ke nan an baka mukami an baka kudi shi ke nan a kashe mutanenka. Shirun ya isa ga al’umma. Kuma ba kyaleka za su yi ba, in sun gama da kai, in ka zama fanko kashe ka za su yi, haka suke yi. Saddam din nan da suka kashe kayansu ne, Gaddafin da suka kashe kayansu ne, duk su suka yi su. Suka kama suka kawar da su.  Kaima in sun gama da kai za su yanka kane, an gama.

ABIN DA YA KUNNO KAI A KASARNAN FA YA SHAFE MU

Na san wannan, munasabar yaumush shuhada muna da magana da yawan gaske ganin cewa; wannan abin da ya kunno kai a kasarnan lallai fa ya shafe mu. Kuma lallai kam fuskantan wannan da duk iyan abin da muke iyawa, aiki ne ga addinin Musulunci. Kuma wanda duk suka kashe a cikinmu sunansa Shahidi! Ban ce muku tunda su suna daukan Bindiga ne, muma zamu dauki Bindiga ne, amma muna da makamai irin namu. To, su zamu dauka insha Allahu.

Allah Ta’ala muna rokonka ka nuna mana Yaumush Shuhada na badi cikin koshin lafiya da yalwar arziki. Allah madaukakin Sarki ka karemu da kariyarka, ka taimakemu da taimakonka ka dora mu birbishin makiya.

Wasallallahu Ala Muhammadin wa’alihid Dayyibinad Dahirin. Wassalamu alaikum warahmatullahi.

Post a Comment

Previous Post Next Post