Netanyahu Ya Yi Shirin Bayar da Rahoto Ga Trump Kan Barazanar Iran

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na shirin gabatar da rahoto ga Shugaban Amurka Donald Trump kan abin da ya kira “barazanar da ke karuwa” da shirin makami mai linzami na Iran ya haifar.

Rahoton NBC News, wanda ya ambato majiyoyi masu tushe, ya bayyana cewa damuwar Tel Aviv ta ƙaru bayan Iran ta fara sake gina wuraren samar da makami mai linzami na ballistic da kuma gyara tsarin tsaron sama da ya lalace a hare-haren baya. Isra’ila na kallon wannan a matsayin batu mafi muhimmanci fiye da shirin nukiliya a halin yanzu.

Sabbin Zaɓuɓɓukan Soji da Netanyahu Zai Gabatar

Majiyoyi sun bayyana cewa Netanyahu zai gabatar da sabbin zaɓuɓɓukan soji ga Trump a wurin shakatawa na Mar-a-Lago, ciki har da yiwuwar Amurka ta shiga kai tsaye ko bayar da tallafi ga wani hari da za a kai wa Iran.
Jami’an Isra’ila sun yi iƙirarin cewa ayyukan Iran barazana ce ga Isra’ila da yankin baki ɗaya, har ma da muradun Amurka. Har ila yau, suna nuna damuwa kan yiwuwar Iran ta sake gina wuraren samar da makamashin nukiliya da suka lalace a baya.

Martanin Trump

A gefe guda, Trump ya bayyana cewa “an lalata karfin nukiliyar Iran gaba ɗaya”, yana mai gargadin cewa duk wani yunkuri na sake gina makami mai linzami ko shirye-shiryen nukiliya za a mayar da martani mai ƙarfi na soja. Duk da haka, ya nuna yiwuwar buɗe kofa ga diflomasiyya.

Post a Comment

Previous Post Next Post