Nafi'u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC



Jam'iyyar ADC a Najeriya ɓangaren Nafiu Bala Gombe ta yi Allah-wadai da yadda ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar tsagin David Mark, Atiku Abubakar yake amfani da sunan jam'iyyar wajen yin abubuwa “ba bisa ƙa'ida ba”.


Cikin wata sanarwa da Nafi'u Bala ya sanya wa hannu a yau 31 ga watan Agusta, ya ce jam'iyyarsu ba za ta lamunci a riƙa amfani da sunanta ba wajen “cin mutuncin Najeriya ba a idon duniya”, inda ta ce hakan cin amanar ƙasa ne da kuma taɓa ƙimarta.


Sanarwar ta ƙara da cewa bai kamata a riƙa “aibanta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu haka kurun ba, duk da cewa ko wane ɗan ƙasa na da 'yancin samun kariya a dokance, amma ya kamata a yi komai bisa doron abubuwan da dokokin Najeriya suka tanada”.


Kwamtin amintattu na jam'iyyar in ji sanarwar ya ce shigar da ƙara a wata ƙasa da Alhaji Atiku Abubakar ya yi kan shugaban Najeriya “rashin kishin ƙasa ne, kuma abin kunya.”


Nafi’u Bala na kalubalantar shugabancin jam’iyyar adawa ta ADC karkashin Sanata David Mark, wadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai yi wa takara a babban zaben kasar na 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post