Sadaukarwar Imam Husaini (A.S.) Ita Ce Madubi Ga Masu Neman 'Yanci – Malam Sidi Manir


 

Malam Sidi Manir ya bayyana cewa sadaukarwar Imam Husaini (A.S.) a filin Karbala ita ce madubi kuma abin koyi ga duk masu neman 'yanci da adalci a faɗin duniya, yana mai cewa irin juriyarsa wajen fuskantar zalunci har yanzu tana ƙarfafa masu gwagwarmayar neman gaskiya.

 

Ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a garin Funtua, Jihar Katsina, a yayin tattakin Arba'in da ake gudanarwa domin tunawa da cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Husaini (A.S.) a ranar Lahadi 2 ga Agustan 2026. 

 

A cewarsa, manufar tattakin ita ce nuna alhini da goyon baya ga iyalan Manzon Allah (SAWW) bisa irin wahalhalu da azabtarwar da suka fuskanta bayan kisan gillar da aka yi wa Imam Husaini (A.S.), iyalan gidan Annabi (SAW) da sahabbansa a filin Karbala. Ya ce bayan wannan mummunan lamari, an ci gaba da gallaza wa matan gidan Annabi (SAW) da ƙananan yaran da suka tsira, inda aka ɗaure su da sarƙoƙi, ana dukansu tare da jan su a cikin hamada cikin matsananciyar ƙishirwa, yunwa da zafin rana, tun daga Iraki har zuwa birnin Dimashƙu da ke ƙasar Siriya.

 

Malam Sidi Manir ya jaddada cewa tunawa da Arba'in ba al'amarin wata mazhaba ba ne, illa al'amari ne da ya shafi Musulunci baki ɗaya. Ya ce malamai na Shi'a da Ahlus Sunna sun ruwaito hadisin da Manzon Allah (SAW) ya ce:

 

"Husaini daga gare ni yake, ni ma daga Husaini nake."

 

Ya bayyana cewa wannan hadisi yana nuna irin matsayi da darajar Imam Husaini (A.S.) a wajen Manzon Allah (SAW), yana mai cewa duk wanda ya cutar da Imam Husaini (A.S.), ya cutar da Manzon Allah (SAW), kuma duk wanda ya tausaya masa, ya tausaya wa Manzon Rahama (SAW).

 

Ya ƙara da cewa wannan ne ya sa Musulmai daga mazhabobin Shi'a da Ahlus Sunna ke gudanar da tarukan tunawa da Arba'in domin tuna irin zaluncin da aka yi wa iyalan Manzon Allah (SAW) da kuma ɗaukar darussa daga abin da ya faru.

 

Dangane da darussan Karbala, Malam Sidi Manir ya ce tsayin daka da juriyar Imam Husaini (A.S.) wajen fuskantar azzalumai su ne suka zama tushen gwagwarmayar dawo da martabar Musulunci a wannan zamani. Ya ce wannan ne ya sa azzaluman duniya ke ɗaukar irin wannan tafarki a matsayin barazana ga mulkinsu.

 

Ya ba da misalin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, gwagwarmayar al'ummar Falasdinu, da kuma gwagwarmayar Harkar Musulunci a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), yana mai cewa duk sun samo ƙarfin gwiwa ne daga darussan Karbala.

 

Ya kuma ce idan aka yi nazari kan yadda Imam Husaini (A.S.) da sahabbansa 72 suka tsaya tsayin daka wajen fuskantar dubban sojojin Yazidu, za a fahimci cewa gaskiya na iya yin nasara duk da ƙarancin mabiya, yana mai nuni da cewa sadaukarwarsu ta tabbatar da abin da ake kira "nasarar jini a kan takobi."

 

A ƙarshe, Malam Sidi Manir ya yi kira ga mahukuntan Nijeriya da su ji tsoron Allah wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, su guji zubar da jinin bayin Allah ba tare da wani haƙƙi ba.

 

Haka kuma ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su rungumi koyarwar Musulunci a matsayin mafita ga matsalolin da ake fuskanta, yana mai cewa siyasar da aka daɗe ana aiwatarwa ba ta samar da mafita mai ɗorewa ba.

 

Ya kammala da cewa bin tafarkin Imam Husaini (A.S.) da kuma amsa kiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na tsayawa kan gaskiya da adalci shi ne hanyar fita daga zalunci da matsalolin da ƙasar nan ke ciki.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post