Baje Kolin Al’adu na Daliban ABU Zaria Ya Kayatar

Daga Idris Umar da Sani Bello, Zaria

Bikin baje kolin kayan al’adu na bana da ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria suka shirya, ya gudana cikin nasara da ban sha’awa a babban filin taro na Kontagora, da ke harabar jami’ar.

Wakilanmu sun shaida mana cewa, kamar yadda aka saba a kowace shekara, ɗaliban jami’ar suna gudanar da bikin nuna al’adunsu  wanda a wannan karon ya zama abin sha’awa ga mahalarta da masu kallo.

A rana ta biyu ta bikin, ɗaliban sun gabatar da gagarumin baje kolin al’adu da ya ƙunshi al’adu daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Baje kolin ya haɗa maza da mata, daga Kaduna da sauran sassan ƙasar, inda mahalarta suka samu damar nuna kayayyakin su na gargajiya da al’adunsu.

Abin da ya fi burgewa shi ne yadda aka gudanar da taron cikin cikakken tsaro, duk da yawan al’ummar da suka halarci wajen.

A yayin taron, masana harkar kasuwancin wayoyin hannu da na’urorin sadarwa, masu gyaran jiki da kwalliyar amare kafin aure, masana harkar ƙamshi da turare, da kuma masu ɗinkin manyan kaya na maza da mata, duk sun samu damar baje kolin sana’o’insu da kayayyakin da suke samarwa.

A ɓangare guda kuma, mawakan da suka shahara wajen nishaɗantar da jama’a sun nuna bajintarsu. 

Daga cikinsu akwai fitaccen mawakin soyayya, Ahmady DJ-HB, da kuma Sir Sodiom, wanda ya nishaɗantar da mahalarta taron ta hanyar wasan barkwanci.

A wannan lokaci, wakilai daga gwamnati ma sun halarci taron, inda suka nuna goyon bayansu tare da sanya wa baje kolin albarka.
An gudanar da wannan gagarumin taro ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Wakilan Ɗalibai (SRC) ta Jami’ar Ahmadu Bello, Comrade Abdulrahman Halliru Saraki.

Bincike ya nuna cewa nasarar gudanar da irin waɗannan taruka na da nasaba da irin gudummawar da Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ahmed, da sauran manyan jami’an gwamnati ke bayarwa wajen tallafa wa harkokin ɗalibai da ci gaban jami’ar.

Haka kuma, ana kallon jagorancin Farfesa Adamu Ahmed a matsayin wani abin da ya taimaka wajen samun nasarori da dama, musamman wajen inganta dangantaka tsakanin jami’ar, gwamnatocin jihohi, da ƙungiyoyi masu zaman kansu a cikin gida da wajen ƙasar nan.

Bikin baje kolin dai zai ci gaba da gudana, inda ake sa ran kammala shi a ranar Lahadi mai zuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post