Dandalin Ɗalibai da Malamai (Academic Forum) na Harkar Musulunci ya bayyana matuƙar damuwa kan wani makirci da ake zargin yana gudana wanda ya shafi ɗaliban Musulmi masu alaƙa da Harkar Musulunci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato. Waɗannan ɗalibai suna fuskantar nau’o’in tsoratarwa da barazana daga hukumomin jami’ar saboda gudanar da karatun Alƙur’ani da ibadu cikin lumana a harabar Babban Masallacin Jibril Aminu da ke babban harabar jami’ar.
A cewar bayanan da muke da su, ɗaliban kan taru a harabar Masallacin Jibril Aminu sau biyu a mako, wato a ranakun Talata da Alhamis bayan Sallar Isha’i, domin karatun Alƙur’ani da addu’o’i. Ana gudanar da waɗannan ayyuka ne ba tare da kawo cikas ga wasu muhimman ayyukan da ake gudanarwa a masallacin ba.
Fiye da shekaru ashirin ke nan waɗannan taruka suke gudana cikin lumana, kuma suna da alaƙa da addini da ilimi.
Abin da ya fi ba mu damuwa shi ne rahotannin da ke cewa wasu mambobin Ƙungiyar Daliban Musulmi ta Najeriya (MSSN) a jami’ar, tare da haɗin gwiwar hukumomin jami’ar, suna ƙulla makircin tilasta hana waɗannan ɗalibai shiga harabar masallacin.
A lokuta da dama, wasu ɗalibai masu tsattsauran ra’ayi, tare da goyon baya da tausayin wasu daga cikin hukumomin jami’ar, sun yi ƙoƙarin kai wa wannan ɗaliban Musulmi hari cikin masallacin. Rashin ganin wani mataki na ladabtarwa da hukumomin jami’ar suka ɗauka kan waɗannan hare-hare na nuna kamar an amince a fakaice da waɗannan ayyuka na rashin bin doka da tashin hankali da ake yi wa abokan karatunsu.
Bayan jerin abubuwan da suka faru, rahotanni sun nuna cewa ɗaliban da abin ya shafa sun kai ƙorafinsu ga hukumomin jami’ar a hukumance, suna neman a binciki lamarin tare da tabbatar da an samar da mafita cikin adalci. Sai dai maimakon a magance muhimman matsalolin da suka gabatar, an ce hukumar jami’ar, ta hannun Shugaban mai kula da lamurran ɗaliban, ta buƙaci ɗaliban su janye daga harabar masallacin.
Wannan mataki ya haifar da manyan tambayoyi game da rashin son kai da hukumomin jami’ar ya kamata su nuna a irin wannan lamari, wanda ya kamata a magance shi cikin adalci kuma bisa ƙa’idojin jami’ar da suka shafi adalci da daidaito tsakanin ɗalibai, musamman batun ’yancin yin ibada.
Wannan matsaya ta nuna wariya da keɓe wasu da shugabancin Ƙungiyar Daliban Musulmi (MSSN) ke ɗauka ta samo asali ne daga zaton cewa ɗaliban da abin ya shafa suna cikin ’yan tsirarun Shi’a, waɗanda a ra’ayinsu ba Musulmai ba ne. A gare su, wannan shi ne dalilin da ya sa bai kamata a bar waɗannan ɗalibai su shiga harabar masallacin ba. Idan wasu ɗalibai masu tsattsauran ra’ayi ne ke da irin wannan matsayar ta ƙuntatacciyar fahimta, to mene ne matsayar hukumomin jami’ar?
Wannan tsarin nuna wariya da ke ƙara samun gindin zama yana ƙara haifar da damuwa game da rashin son kai na hukumomin jami’ar kan batutuwan addini da kuma tsarin fahimtar ɗalibai. Saboda haka, ana iya yin wata muhimmiyar tambaya game da yanayin addini da mazhaba na jami’ar kanta: Shin Jami’ar Usmanu Danfodiyo jami’a ce ta wata mazhabar Musulunci ta musamman, ko kuma jami’ar gwamnati ce da ke yi wa ɗalibai daga mabambantan addinai da sauran al’ummomi hidima?
Idan aka yi la’akari da matsayar MSSN a jami’ar mai cike da bambancin mazhaba da kuma tsaurin ra’ayi, dole ne a tambayi ko ƙungiyar tana wakiltar ɗaliban Musulmi gaba ɗaya, ko kuma an tsara ta ne da gangan domin tilasta fahimtarta ta addini mai tsauri ga sauran ƙungiyoyin ɗaliban Musulmi.
Waɗannan ba tambayoyin ilimin addini kawai ba ne, sai dai damuwa ce da ta shafi muhimman ƙa’idojin adalci, daidaita mu’amala, ’yancin addini da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma a cikin wata cibiyar ilimi da ya kamata ta kasance mai karɓar bambance-bambance da ra’ayoyi iri-iri.
Academic Forum na son ta bayyana a fili cewa ɗalibanmu ba sa neman wata gata ta musamman. Abin da suke nema shi ne a ɗauke su bisa haƙiƙanin matsayinsu: ɗalibai Musulmi da suka yi rajista bisa doka a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, kuma waɗanda suke cikin al’ummar jami’ar. Abin da suke nema kawai shi ne a ba su damar ci gaba da gudanar da karatun Alƙur’ani da addu’o’insu cikin lumana a wurin da ya dace a cikin masallacin, kamar yadda suka kasance suna yi tsawon shekaru da dama.
Abu ne mai matuƙar tayar da hankali idan za a hana ɗalibai shiga wurin ibada kawai saboda fahimtarsu game da Musulunci ta bambanta da ta wata ƙungiya.
Ya kamata jami’a ta kasance wurin da ake magance bambance-bambancen ra’ayi ta hanyar tattaunawa, haƙuri, bin ƙa’idoji da mutunta juna, ba ta hanyar tsoratarwa, keɓe wasu, ko amfani da ƙarfin hukuma wajen danne wasu — ko ’yan tsiraru ba — domin fifita wata ƙungiya, waɗanda ake ganin masu rinjaye.
Saboda haka, muna kira ga mahukuntan Jami’ar Usmanu Danfodiyo da su ɗauki matakin gaggawa wajen tabbatar da cewa babu wani ɗalibi da za a yi wa wariyar addini, tsoratarwa ko cin zarafi saboda kasancewarsa mamba ko mai alaƙa da wata fahimtar Musulunci. Haka kuma, muna kira gare su da su mutunta bambance-bambancen da ke tsakanin ɗaliban Musulmi, tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna, ƙiyayya ko rikici da ba dole ba a cikin al’ummar jami’ar.
Haka nan muna kira ga hukumomin jami’ar da abin ya shafa, hukumomin da ke kula da harkokin ilimi, ƙungiyoyin fararen hula, da dukkan masu kishin adalci da zaman lafiya da su mai da hankali kan wannan lamari tare da tabbatar da an kare haƙƙoƙi da mutuncin ɗaliban da abin ya shafa.
Jami’o’i dole ne su kasance wuraren neman ilimi, ’yancin tunani, adalci da zaman lafiya, ba wuraren da za a bar wata ƙungiya ta yanke hukuncin wanda ya cancanci gudanar da addininsa da wanda bai cancanta ba.
Sa hannu:
Muhammad Jawad
A madadin: Academic Forum na Harkar Musulunci
Ƙarƙashin jagorancin Mai Girma, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
10 ga Agusta, 2026
Post a Comment