Saƙon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ayatullah Sayyid Mujtaba Al-Husayni Al-Khamene'i


Dangane da cika shekara guda da buɗe zaman farko na Majalisar Shawarar Musulunci ta goma sha biyu da kuma fara shekara ta uku ta ayyukanta

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai

Jagoran Addinin Musulunci a Iran, Ayatullah Sayyid Mujtaba al-Husayni al-Khamene'i, ya bayyana cewa maƙiyan Iran suna ƙoƙarin tayar da rikice-rikicen zamantakewa da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'umma. Ya ce suna amfani da matsin tattalin arziki, killacewar yaɗa labarai da matsin lambar siyasa domin raunana haɗin kan jama'a, da nufin rama shan kaye da suka sha a fagen yaƙi tare da karya ƙarfin zuciyar al'ummar Iran.

Ya jaddada cewa wajibi ne a kan duk masu kishin Musulunci, Juyin Juya Halin Musulunci, 'yancin kai da ɗaukakar Iran su yi iya ƙoƙarinsu wajen kare haɗin kai da daidaiton al'umma, tare da hana ko da ƙananan sabani rikidewa zuwa rikici da rarrabuwar kawuna. Ya ce ya kamata kowa ya zama abin koyi wajen nuna haɗin kai, fahimtar juna da kishin ƙasa ta hanyar magana da aiki.

Taya murna da godiya

Ina taya al'ummar Iran da dukkan 'yan Majalisar Shawarar Musulunci murnar zagayowar buɗe zaman farko na Majalisar da kuma zuwan Babbar Sallah mai albarka. Haka nan, ina miƙa godiyata ga dukkan 'yan majalisa, musamman shugaban Majalisar, Dakta Muhammad Baqir Qalibaf, bisa ƙoƙarinsu wajen yi wa ƙasa hidima da ɗaukaka.

Matsayin Majalisar Shawarar Musulunci

Hakika Majalisar Shawarar Musulunci ita ce madubin hikimar al'umma, alamar ikon jama'a na addini, kuma ginshiƙi ne na doka da tsari a Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tana taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da muradun jama'a da kare maslaharsu.

Abubuwan da suka faru a watannin baya sun sake bayyana ƙarfin imani, jajircewa da haɗin kan al'ummar Iran. Wannan ya nuna wayewa da bajintar jama'a, kuma ya ƙara ɗora wa wakilan jama'a alhakin tsara ayyukansu bisa bukatun al'umma da makomar ƙasa.

Saboda haka, ya kamata 'yan majalisa su ƙara himma wajen tsara dokoki masu amfani da kuma sa ido kan yadda ake gudanar da al'amuran ƙasa domin tabbatar da ci gaba da ɗorewar Iran Musulunci.

Nauyin wakilai

Matsayin wakilci matsayi ne mai girma wanda yake a sahun gaba wajen ciyar da ƙasa gaba. Don haka ya dace wakilan jama'a su dogara ga Allah Maɗaukaki, tare da neman taimako da albarkar Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), su kuma kiyaye amanar jinin shahidai waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare ƙasa.

Haka nan, ya kamata su yi aiki tare da sauran hukumomin gwamnati wajen ƙarfafa haɗin kai, kare ikon majalisar dokoki, da kuma magance matsalolin jama'a musamman waɗanda suka shafi tattalin arziki da rayuwar yau da kullum.

Ya kamata a mai da hankali kan:

  • Ƙarfafa samar da kayayyaki da ayyukan yi;
  • Bunƙasa ilimi da masana'antu;
  • Inganta tarbiyya da ɗabi'a;
  • Yaƙi da cin hanci da rashawa;
  • Rage hauhawar farashi da tsadar rayuwa;
  • Da kuma yaƙi da talauci.

Dokoki masu anfani ga jama'a

Dokokin majalisa ya kamata su kasance masu alaƙa kai tsaye da muhimman bukatun ƙasa da na jama'a. Haka kuma su kasance masu ƙarfafa fata da kyakkyawan hangen nesa game da makomar ƙasa.

Al'umma na buƙatar ganin alamomin ci gaba da kwanciyar hankali domin su samu damar tsara rayuwarsu cikin tabbaci. Saboda haka, wakilai za su iya amfani da matsayinsu, dokokinsu da jawabansu wajen mayar da majalisa cibiyar yaɗa fata da ƙarfafa guiwar jama'a.

Har ila yau, ya kamata a ƙara mai da hankali kan manufar "Tattalin Arzikin Juriya", ta hanyar:

  • Rage hauhawar farashi;
  • Sauƙaƙa harkokin gudanarwa;
  • Ƙara samar da kayayyaki;
  • Inganta shirye-shiryen ci gaban ƙasa;
  • Da kuma sake gina abubuwan da suka lalace sakamakon yaƙe-yaƙe da takunkuman da aka kakabawa ƙasar.

Muhimman siffofin wakili nagari

Domin sauke nauyin wakilci yadda ya kamata, ya zama wajibi wakilai su kasance masu:

  • Tsoron Allah;
  • Fahimtar abubuwan fifiko;
  • Yin nazari mai zurfi kafin yanke hukunci;
  • Rayuwa irin ta talakawa;
  • Kusanci da jama'a;
  • Yaƙi da cin hanci da rashawa;
  • Fifita muradun ƙasa a kan son rai ko muradun jam'iyya;
  • Kula da diflomasiyyar majalisa;
  • Jarumta da faɗin gaskiya;
  • Da kuma anfani da ilimi da fasaha wajen fuskantar sabbin ƙalubale.

Muhimmancin haɗin kan ƙasa

Daya daga cikin manyan ni'imomin da Allah Ya yi wa Iran ita ce haɗin kai da daidaituwar al'umma. Wannan haɗin kai ya taimaka wajen fuskantar manyan ƙalubale da matsin lamba daga maƙiya.

Saboda haka, wajibi ne ga dukkan jama'a, musamman masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da tunani, su kiyaye wannan ni'ima ta hanyar nisantar rikice-rikicen siyasa marasa amfani da kuma gujewa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kawuna.

Lallai maƙiya suna ƙoƙarin amfani da matsin tattalin arziki, yaɗa farfaganda da matsin siyasa domin tayar da sabani a cikin al'umma. Don haka, duk mai kishin Musulunci, Juyin Juya Halin Musulunci, 'yancin kai da martabar Iran ya kamata ya ƙara ƙaimi wajen kare haɗin kai da zaman lafiya.

Bai kamata a bari bambance-bambancen ra'ayi su rikide zuwa rikici da rarrabuwar kawuna ba. Maimakon haka, kowa ya zama abin koyi wajen nuna jituwa da haɗin kai ta hanyar magana da aiki.

Kammalawa

Ina yi muku fatan samun nasara wajen sauke wannan babban nauyi na wakiltar ƙasa mai albarka da al'umma masu jarumta, waɗanda suka fuskanci zalunci da matsin lamba daga maƙiya cikin juriya da ƙarfi.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ku dacewa da nasara, Ya sa albarkar Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa) ta kasance tare da ku, Ya shiryar da ku zuwa ga abin da yake alheri ga ƙasa da al'umma.

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

Post a Comment

Previous Post Next Post