An shirya bikin bankwana na kwanaki uku domin tunawa da marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

 


Majalisar Daidaita Ayyukan Raya Addinin Musulunci ta sanar cewa za a gudanar da bikin bankwana na jama’a na kwanaki uku a babban filin ibada na Grand Mosalla da ke babban birnin Iran, wato Tehran.

A cewar sanarwar da majalisar ta fitar a ranar Laraba, bikin zai fara ne da ƙarfe 10:00 na dare agogon kasar, kuma zai ci gaba na tsawon kwanaki uku.

An yi kira ga jama’a da su halarci domin girmama “shahidan jagora kuma babban kwamandan juyin juya halin Musulunci”. An kuma mika ta’aziyya ga al’ummar Musulmi, tare da kira ga dukkan sassan al’ummar Iran — maza da mata, matasa da manya, malamai, dalibai, ma’aikata, manoma da sauran jama’a — da su halarci bikin.

Sanarwar ta kara da cewa yawan halarta zai nuna hadin kan kasa, biyayya ga manufofin juyin juya hali, da kuma tsayin daka wajen fuskantar abokan adawa daga waje.

Majalisar ta bayyana Ayatollah Khamenei a matsayin bawan Allah da ya sadaukar da rayuwarsa wajen karfafa “tsantsar addinin Musulunci na Muhammadiyya”, kare ‘yancin kai da martabar Iran, tare da karfafa bangaren gwagwarmaya.

An bayyana cewa an tsara wasu shirye-shirye na musamman na zaman makoki na kwanaki ukun.

Haka kuma, ana ci gaba da shirye-shiryen jerin gwanon jana’izar, kuma za a fitar da karin bayanai idan an kammala.

Majalisar ta ce tana sa ran dimbin jama’a za su halarta domin isar da sako har ma bayan iyakokin Iran, inda ta nuna fatan goyon baya ga magoya baya tare da gargadi ga abokan adawa cewa hanyar gwagwarmaya da adalci za ta ci gaba.

A ranar Asabar da safe, an kai hari kan gidan Ayatollah Khamenei a Tehran, harin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan uwansa da dama, ciki har da ‘yarsa, surukinsa, da jikansa.

An sanar da shahadar sa ne a farkon safiyar Lahadi.

Post a Comment

Previous Post Next Post