Iran Ta Kaddamar da Manyan Atisayen Sojojin Ruwa a Tekun Fasha

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da gagarumin atisayen sojojin ruwa a Tekun Fasha, wanda aka sanya wa suna bayan Shahid Haj Mohammad Nazeri, domin nuna ƙarfi da shirin kare yankin ƙasar.

A cikin bayanan da hukumomin tsaro suka fitar, an bayyana cewa rundunonin sojojin ruwa sun aika gargadi bayyanannu ga jiragen ruwan Amurka da ke cikin yankin yayin gudanar da atisayen. Iran ta ce wannan mataki na nuni ne da “cikakken ikon ta na kare yankinta da martaba tsaron ruwa.”

Atisayen ya haÉ—a da amfani da ingantattun tsarin tsaron sama na zamani irin su Nawab, Majid da Mithaq, waÉ—anda aka gwada su a yanayin yaki na lantarki domin tantance inganci da saurin mayar da martani.

Haka kuma, rundunar sojojin ruwa ta IRGC ta bayyana cewa manufofin atisayen sun haɗa da nuna ƙarfin fada, gwada sababbin kayan aikin tsaro da dabarun kai farmaki, da kuma tabbatar da cewa Iran na da cikakkiyar kwarewa wajen kare muradun ta a tekun Fasha.

Hukumomin tsaron Iran sun ce atisayen ya kasance wani bangare na shirin ci gaba da horarwa da nuna shirin kare yankin Æ™asar a kowane lokaci. 

Post a Comment

Previous Post Next Post