Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya wallafa cewa; a ranar Alhamis, 13 ga Jimadal Thani 1447 (4/12/2025), wanda ya dace da kwanaki bakwai da rasuwar Shaikh Dahiru Usman Bauchi, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya tura da tagawar musamman don yin ta'aziyya ga iyalai da almajiransa.
Sayyid Badamasi Yaqoub, wanda yake ƙani shaƙiƙi ga Jagora, ya bayyana ta'aziyyar Jagora (H) ga iyalan Shehin, tare da bayyana rashinsa a matsayin wani bango ga duniya, a matsayinsa na mahaddacin Alkur'ani, kuma mai hidima ga Alkur'ani a tsawon rayuwarsa.
Ta bangaren iyalan mamacin, Khalifa Shaikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya nuna godiyarsu ga ta'aziyyar, tare da bayyana rashin Shehin a matsayin abin yi ta'aziyya wa juna gabadaya. Ya bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky da marigayi Shaikh Dahiru Bauchi, inda ya bada misali da irin lokutan da Shaikh Zakzaky ya rika ziyartan Shehi a baya, har Shehi kan gabatar da shi ya ja su Sallah.
Tawagar ta hada da babban ɗan Jagora (H), Sayyid Muhammad Zakzaky, da 'yan uwan Jagora na jini, tare da ba'adin wakilan 'yan uwa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
An gabatar da addu'o'i na musamman ga Shehin, dafatan Allah Ta'ala Ya jaddada masa rahama da jinkai.
Post a Comment