Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi kaca-kaca da sanarwar da shugabannin Majalisar Haɗin Kan Gulf (GCC) suka fitar dangane da ikirarin da aka yi kan tsibiran Iran guda uku.
Kakakin ma’aikatar, Ismail Baghaei, ya nuna baƙin ciki game da dagewar GCC kan maimaita ikirarin da ya kira “marasa tushe”, waɗanda Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ke yi kan tsibiran Abu Musa, Greater Tunb da Lesser Tunb. Baghaei ya ce batutuwan da aka ambata a sanarwar ƙarshe ta taron kolin GCC karo na 46 “ba su da inganci”, yana mai jaddada cewa waɗannan tsibiran “muhaimmin ɓangare ne na yankin Iran tun ƙarni da dama.”
Baghaei ya jaddada cewa maimaita ikirari ba ya canza gaskiyar tarihi ko haifar da wani haƙƙin doka ga masu da’awa. Ya ce duk wani yunƙuri da ya sabawa ka’idojin mutunta iyakokin ƙasashe da kyakkyawar maƙwabtaka “bai dace ba kuma ba zai amfanar da yankin ba.”
Kakakin ya kuma nanata manufar Iran ta bunƙasa kyakkyawar maƙwabtaka da haɓaka haɗin gwiwa da ƙasashen yankin don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali. Ya yi kira ga UAE da Majalisar Haɗin Kan Gulf da su guji matakan da ka iya tayar da rigima ko kassara tattaunawa.
A wani bangare, Baghaei ya tabbatar da haƙƙin Iran kan rijiyar man Arash, yana mai cewa ikirarin da wasu ƙasashe ke yi a kai “ba su da wata hujja ta doka.” Ya ce fitar da sanarwa ko maimaita ikirari ba zai haifar da wani haƙƙi ga Kuwait ba, inda ya jaddada cewa hanyar warware batun ita ce ta hanyar tattaunawa kai tsaye, haɗin gwiwa da gina yanayi mai kyau.
A ƙarshe, Baghaei ya nanata cewa kalaman siyasa ba sa canza gaskiyar cewa tsibiran uku mallakin Iran ne.
Post a Comment