Yadda Aka Gabatar Da Zagayen Muzaharar Mauludi A Garin Firji Dake Jihar Jigawa

 


Daga Wakilinmu Naseer

A ranar Asabar 2/5/1447 25/10/2025 'Yan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin firji suka gabatar da zagayen muzaharar Mauludin Manzon Allah (Saww) kamar yadda aka saba gabatarwa du shekara. An taso da muzaharar ne daga arewa primary school firji sai aka biyo da ita ta babbn titin daya nufi Kano da daura bayan daukar wasu mintuna ana tafiya sai aka ketara da ita ta hayin Yamma akabi wasu 'yan lunguna sannan aka dawo da ita ta dayan ketaran na gabas nan ma anshiga lungu da sako na ketaran, inda a karshe sai aka kawota kofar fadar hakimin garin dake bakin titi. Bayan is wurin rufewa 'yan fudiyoyi sun gabatar da da faretin girmama ga Manzon Allah (Saww) a karshe sai aka gabatar da malam Kabir Dambatta wanda shine ya gabatar da jawabin rufewa Alhamdulillah any lafiya an kammala lafiya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post