Daga Bashir Adam Bomo
A ranar 20/10/2025 Litinin ne Yan uwa almajiran Sayyed zakzaky (H) Dake anguwan Mai Gamo Suka Gabatar da maulidin Manzon Allah (Saww). Wanda Suka Saba Duk shekara. Bayan Bude Taron da Addua da karatun kur'ani Mai girma. Sannan 'yan Fareti suka taka fareti Mai Ban sha'awa a wurin. Shaikh Aliyu Tirmizi Kaduna ya fara jawabi da godiya ga Allah (SWT) ya yi gaisuwa ga Annabi (S) da iyalan gidansa tsarkaka.
Daga nan ya cigaba da cewa; ba a kwatanta Annabi (S) da duk wani Annabi kuma kowanne Annabi sai ya yi imani da Annabi Muhammad (s) sannan yake samun Annabci. Yadda suke imani da Allah (T) haka Suke imani da Annabi sannan a ba shi Annabci ya zama Annabi. An tambayi Imam Ja'afar Assadiq (AS) cewa taya Annabawa za su taimakawa Annabi (S). Sai ya ce kowanne Annabi a lokacinsa zai rika gayawa mutanensa cewa a qarshe akwai Annabin da zai zo shi ne Annabin Annabawa shugaban Annabawa (SAWW).
Saboda haka ba a haďa Annabi da sauran Annabawa (as). Na taba sawa ďana suna Baqeer wani sai ya ce min Baqeer kuma ku dai akwai ku da kwashe kwashe, ina kuma kuka samo suna Baqeer? Sannan shehin Malamin haka ya cigaba da kawo darajojin Manzon Allah (S) da ahalinsa. Inda daga karshe ya ce Annabi yafi komai da komai na duniyar nan. Sannan ba a bada wani misalin da wata daraja na shi da har za a hada shi da wani abu. Annabi Rahma ba abin wasa bane. Daga karshe an yi addu'a, an tashi lafiya.

Post a Comment