Shaikh Zakzaky Ya Bayyana Matsayarsa Kan Rikicin Sudan


A wata hira da kafar watsa labarai ta iran press ta yi da jagoran harkar musulunci a najeriya shaikh Ibrahim zakzaki yayi tir da ci gaba da kashe mutane da ake yi a kasar sudan inda kungiyar RSF ta kasashe sama da mutane 2000 a garin el-fishar, ya zargi kasar hadaddiyar daular larabawa da ruruta wutar yaki a madadin kasashen masu girma na duniya. 

Yakin basasar dake ci gaba da gudana a kasar sudan ya dauki mummunan yanayi yayin  da kungiyoyin masu samun goyon bayan kasashen waje ke kara kai hare-hare kan fararen hula da basu ji ba basu gani ba, bayanan na shaikh zakzaki sun kara haskaka yanayin siyasar da ke mayar da kasashen afrika fagen yaki don rarrabasu, Har ila yau shaikh zakzaki yayi tir da mummunan rikicin da ya keta kasar sudan din gida biyu, kana ya jaddada cewa dukkan dakarun sojin kasar sudan da kuma kungiyar RSF yan kasar Sudan ne wadanda suke aiwatar da agenda kasashen waje, yace lamari ne mai taba zuciya a ce dan uwa yana kashe dan uwansa kawai don kare masalar wasu a waje, Yace kasar hadaddiyar daular larabawa tana aiki ne a madadin kasashen yamma kuma matukar baa yanke hannun kasashen waje ba to yaki ba zai tsaya ba, fararen hula ne kawai zasu ci gaba da zama cikin mawuyacin hali.

Post a Comment

Previous Post Next Post