Mauludin Halƙar Amirul Mu'uminin (Ƴar Shantali)

 


A cigaba da gudanar da Mauludin Manzon Allah (s a w) na halƙoƙi, yau Lahadi 04-Jimada Auwal-1447 ƴan uwa na halƙar ƴar shantali (da'irar Shinkafi) sun gabatar da taron bukin murna da haihuwar fiyayyen halitta (s a w). Taron ya samu halartar dimbin al'ummar Shinkafi yayi da shehin Zawiyyar Mabera Malam Rabiu ya kasance baƙo me jawabi, wanda ya gabatar da maudu'i me taken; DARAJOJI DA MU'UJIZOZIN MANZON ALLAH (S A W). 

A cikin jawabin shehin yake cewa "Bayahuden yace da Manzon Allah ka dawo da dare, sannan wata ya bayyana, kuma ya tsage biyu. Se Manzon (s a w) yaje dutsen Abu Ƙubaiz yayi Sallah raka biyu ya roki Allah, take Jibrilu yazo yace da ma'aiki (s a w) Allah ya lamunce ma duwatsu da iska, nan take dare ya haɗu se ga wata ya bayyana kuma ya tsagen. nan take bayahude yace Ashhadu-alla'ilah illallah..." Bayan kammala jawabin Shehin, wakilin ƴan uwa Malam Ƙasim Shehu ya gabatar da ta'aliƙi, inda a cikin jawabin sa yake cewa "yanzu muna cikin wani shu'umin zamani wanda wasu shu'umman mutane suke musun abubuwan da suke tabbatattu, ba wanda suke kaiwa hari se Ma'aiki (s a w), duk wani abu wanda yake reni se su jingina shi ga (s a w), abunda ya zama daukaka kuma se su tunkuɗe sa akan Manzon Allah (s a w)" A ƙarshe ƴan uwa na halƙar sun bada kyautar tallafin kuɗi kimanin Naira dubu ɗari da goma(110k) domin cigaba da haɓaka karatun Fudiyya.



#MAULUD1447

Post a Comment

Previous Post Next Post