Daga Mardiyyah Kabiru
A ranar 25/10/2025 daliban Madarasatul Fudiyya Bomo dake karamar hukumar Sabon gari Zaria suka gudanar da gagarumin mauludin fiyayyen halitta Manzon Allah (SAWW) wanda suka suka gabatarwa duk shekara a muhallin Fudiyyah Bomo. Wannan shekarar ma cikin ikon Allah sun gudanar inda aka gabatar da abubuwa masu ban sha’awa da ilimantarwa. Bayan bude taro da addua an gabatar an kamsasa wajen ta ayoyin daga cikin Alqur'ani mai girma. Sannan daliban sun gabatar da kayatacciyar tamsiliyya(drama)wasan kwaikwayo kenan inda sukai nuna game da anfanin neman ilmi ga matasa. Sannan sha'iraii sun kayatan wajen da gwalagwalan baitocinsu ga fiyayyen halitta Manzon Allah (SAWW).
Babban Malamin daya samu halartan wajen Mal Lukman Alfa Samaru. Daga Cikin Jawabin nasa inda yake cewa; a nasa ran kai da kake amsa suna na masoyi kuma mabiyin Manzon Allah (SAWW) kayi koyi da halayensa. Babu wani abinda ya dace da wannan al'ummah face son Manzon Allah (SAWW).Manzon Allah (SAWW) shi ne tsarkakekken da yafi kowa tsarki cikin halittun ubangiji. Manzon Allah (SAWW) ya kasance yana raya darensa ne da ibadat. Manzon Allah wani mizanine ko ma'auni ga al'umma baki daya. Daga karshe ya karkare da jaddada soyyayarsa ga Manzon Allah (SAWW)da iyalan gidansa. Sannan an bada kyauta ga masu wadannan sunan :
Muhammadu
Aminatu
Abdullahi
Daga karshe wakilin Yan uwa na samaru Malam Muhammad Barau Samaru yayi Jawabin godiya. Da Rufe taro da addua.

Post a Comment