FAƊAKARWA
Bismillahir Rahamanir Raheem.
A 'yan kwanakin nan, wasu da muke kyautata zaton 'yan uwa ne, kuma masu kyakkyawar nufi, suna amfani da fasahar' Artificial intelligence (AI)' suna ƙirƙiran hotuna iri daban-daban, suna yaɗawa a kafafen sadarwa. Hotunan na ɗauke da wasu alamomin Harka Islamiyya, kamar hoton Jagora (H) a cikin wasu gurare, irin su dakin gwaje-gwaje, ko dakin yaƙi, ko filin daga da sauransu. Ko kuma su kirkiri hoton wasu mutane su saka musu kayan soja, suna tirenin a wani waje, tare da sanya musu Logo din Harisawa.
Ko kuma canzawa hoton Jagora (H) fasali, zuwa wani abu mai kama da wargi da wasa, tare da sanya Logo din Ofishin Jagora a jikin hoton, sai ya zama kamar Ofis din ne ya fitar da hoton a haka. Lallai wadannan ayyukan ba abu ne kyakkyawa ba, ba kuma sunansa cigaba ba, abu ne wanda yake da illa, kama daga rashin wayewa, da mayar da Jagora (H) ko Harka Islamiyya a matsayin wasa da wargi a idon duniya, zuwa baiwa maƙiya iri daban-daban kafar cutar da Harka ta fuskoki daban-daban yanzu ko nan gaba. Bisa haka, muna kira ga 'yan uwa da suke yin irin wannan, su bari. Waɗanda suka yi a baya, su goge a shafukansu.
Har ya zama in an ga wani ya cigaba ƙirƙira ko yaɗa irin waɗannan zanen, an san cewa da wata mummunar manufa yake yin hakan a nan gaba, kuma 'yan uwa ba za su biye masa ba. Muna fatan Matasan Harka Islamiyya, - ma'abota basira da sadaukarwa - za su duƙufa wajen binciken hanyoyin samar da cigaba na haƙiƙa ga tafarkin gwagwarmaya, ba tare da shagaltuwa da abubuwan da suka fi kama da wasa ba.
H-Central.
— Hurrasul Harakatil Islamiyya
29/4/1447 / 22/10/2025
Post a Comment