A jiya Lahadi ne, mambobin Kwamitin Ilimi na Harisawan Harkar Musulunci a ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) suka kammala Dauran Karatu na tsawon kwanaki uku da suka shiga daga ranar Alhamis 13 zuwa Lahadi 16 ga watan Nuwambar 2025 a garin Kano.
Dauran, wanda kwamitin Ilimi na Hurras Central ta shirya, ya ƙunshi wakilan kwamitin ilimin daga dukkan Zones 14, da Unitoci 45 da ake da su a faɗin aikin na Harisanci.
An gudanar da karatuttuka akan bangarori daban-daban na ilimin addini da suka hada da Fiqihu, Akhlaq, da kuma abinda ake kira ilimin boko, sannan an bayyana sabon tsare-tsaren kwamitin na ilimi wanda ake fatan dukkan Harisawa za su ɗoru a kansa.
Da yake jawabin rufewa, wakilin Hurras Central a wajen taron, Saifullahi M. Kabir, ya ja hankalin wakilan akan muhimmancin fahimtar kansu a matsayin Mas'ulai a wannan ɓangaren. Inda ya yi bita akan siffofin Mas'uliy nagari, tare da jaddada musu fatan da ake da shi daga ɓangaren ilimin Harisanci nan da ƙanƙanin lokaci.
Harwayau, ya lurantar da su, muhimmancin bibiyan da samun cikakkiyar masaniya akan siyasar duniya, da nazari akan duniyar Muqawama domin fahimtar kulen da ke gabanmu, da kuma wajabcin ƙara lizimtar Jagora (H) don fahimtar haƙiƙanin hadafin Haraka Islamiyya, da yadda hanyoyin cimma hadafin (policies) suke caccanzawa. Inda yace, rashin lizimtar Jagora (H) ne kan sa mutum ya riƙa ruɗewa ko shiga shubha akan matsayoya da Jagorancin Harkan ke ɗauka a kowane lokaci.

Post a Comment