Daga: Bashir Adam
’Yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Ya’qub Al-Zakzaky (H) na Bomo sun gudanar da Majalisul Azā na jaje domin tunawa da wafatin Sayyada Fatima Az-Zahra (AS) a muhallin Fudiyya Bomo, Zariya.
Majalisin, wanda aka yi a ƙarƙashin taken:
“Sayyada Zahra (AS): Sanfurin Turjiya ga Zalunci da Neman ’Yanci,”
ya gudana cikin nutsuwa tare da halartar mabiya mazhabar Ahlul Baiti.
Bayan kammala karatun azā, Sister Zahra’u Kabiru Bomo ta gabatar da takaitaccen jawabi kan shahadar Sayyada Zahra (AS). A cikin bayaninta, ta yi tsokaci kan gwagwarmayar da Sayyada Zahra ta sha bayan rasuwar mahaifinta, Manzon Allah (SAW), har zuwa yanayin da ya kai ga shahadarta.
25/11/2025

Post a Comment