DANDALIN MATASA SUN GABATAR DA TARON KARAWA JUNA SANI GA WAKILAN ƁANGARI A YANKIN SOBA



Daga Journalist Muhammad Ahmad

A safiyar Lahadi, 26—10—2025, Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) na yankin Amirul Muminin a garin Soba sun gudanar da taron ƙara wa juna sani wanda ya haɗa wakilai daga garuruwa daban-daban na yankin Soba, Jihar Kaduna, domin ƙwaƙƙwafa tunani da sanin makamar aiki. 

Taron ya fara gudana ne da jawabin Malam Yahaya Salisu Barwa, wanda ya yi jawabi kan "Gudanarwa" da kuma yadda ya kamata wakilai su tafiyar da al’amuran wakilci cikin adalci da haƙuri. A cikin jawabinsa, Malam Yahaya, ya jawo hankalin wakilai da su kasance masu tsayuwa akan gaskiya, haƙuri, da hadin kai a yayin gudanar da ayyukansu, yana mai cewa: “Duk da cewa wakilai sun fito daga ɓangarori daban-daban, wajibi ne su haɗu a kan manufa guda domin ci gaban Dandalin Matasa.” Bayan haka, Yusuf Ahmad ya gabatar da jerin kwamitocin da ke cikin Dandalin Matasa da kuma wakilan da ke jagorantar su a Soba Unit. 

Daga bisani kuma, Dan uwa Sani Abdurrahman Bai’a ya yi jawabi mai ƙarfafawa ga wakilai, inda ya jaddada bukatar bin irshadin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), yana mai cewa: “Jagora (H) da kansa ne ya umarci matasa da su samar da tsarin jagoranci mai nagarta da tsari guda, domin gudanar da ayyukan Dandalin Matasa cikin tsari da natsuwa.” Ya ƙara da kira ga matasa da su zabura wajen aiwatar da ayyukan Dandalin domin cimma manufar haɗin kai da tsarkake al’umma. Bayan kammala taron, an gudanar da sallar jam’i, sannan aka ci abinci tare da yin addu’a kafin a sallami mahalarta taron.


Amirul Muminin Zone (Zariya)


 

Post a Comment

Previous Post Next Post