Farfesa Maqari ya Kai Ziyarar Haɗin Kan Malamai ga Sheikh Zakzaky a Abuja

 


A wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai da mabiya addinin Musulunci, Farfesa Ibraheem Maqari tare da tawagarsa sun kai ziyara ga Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a gidansa da ke Abuja, ranar Lahadi 2 ga watan Nuwamba 2025. A cikin tawagar Malaman akwai Shaikh Nura Khalid da sauran Malamai.

Ziyarar ta mayar da hankali ne kan buƙatar haɗin kai, fahimtar juna da kusanci a tsakanin malamai daga bangarori daban-daban na addinin Musulunci, domin ƙarfafa zumunci da kawar da sabani a tsakanin al’umma.

Rahoton da ya fito ne daga ofishin Jagora, ya labarta cewa Sheikh Zakzaky (H) ya yi maraba da wannan yunƙuri, inda ya yabawa ƙoƙarin Farfesa Maqari da tawagarsa wajen ganin an samu haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin malamai da mabiya addini.

A yayin ziyarar, Sheikh Zakzaky ya ƙarfafa buƙatar ci gaba da irin waɗannan tattaunawa, yana mai addu’ar alkhairi da nasara ga dukkanin ɓangarorin da ke neman haɗin kai da fahimtar juna.

Ziyarar ta Farfesa Maqari ta zo a lokaci mai muhimmanci, inda ake ci gaba da kira ga haɗin kan Musulmi a fadin duniya da kuma addu’a ga al’ummar Falasdinu da shahidan Musulunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post