“Nawa ne kuɗin abincin da zaku yini ku kwana? Zan biya.” Wannan kalamai ne na wani bawan Allah da ya tarar da ’yan uwa suna gudanar da Muzaharar Maulidi a cikin wannan ƙasar gumin daji.
Alhamdulillah, cikin ikon Allah da damarSa, wasu ’yan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) daga garin Gombi, Jihar Adamawa, sun isa wannan yankin domin amsa gayyatar wani bawan Allah da ya bukaci a gudanar da Maulidi a wannan daji.
Dajin Dagareji ya shahara a wajen mazauna yankin Gombi (LGA) da kuma mutanen garin Son (LGA). Asalin samuwar wannan daji ya samo asali ne daga masaukin manoma, amma yanzu ana kiyasta mazauna yankin sun haura mutane 1,000.
A yayin gudanar da Muzaharar, mazauna ƙauyen sun nuna matuƙar farin ciki da godiya game da Da’awar Sayyid Zakzaky (H). Da yawa daga cikinsu sun bayyana jin daɗinsu da kalmomin:
“Wallahi abin ba a magana.”
Sun yi addu’a ga Sayyid Zakzaky (H), tare da cewa, “In Allah ya yarda yanzu muka fara.”

Post a Comment