*Ta Danganta Nasararta Ga Tarbiyya da Jagorancin Sayyid Zakzaky (H)
Wata ɗaliba mai suna Batuola Muhammad Siraj ta bayyana farin cikinta bayan ta samu lambar yabo ta “The Most Full Hijabi Wearer” a sashen karatunta, inda ta nuna godiya ga Allah da kuma masu taimaka mata wajen cimma wannan nasara.
A cikin saƙon ta da ta wallafa a shafin Facebook, Batuola ta ce wannan nasara ba na ta kaɗai bace, domin nasarar na wakiltar irin ɗimbin darussa, jagoranci da ta samu daga jagoranta kuma malamin ta, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
Ɗalibar ta yi addu’ar Allah Ya kare shi, Ya ƙara masa basira, tare da sakayya ta alheri bisa ƙoƙarinsa na tarbiyyantar da al’umma
Ta kuma mika saƙon godiya ga iyayenta bisa ƙauna, addu’o’i da goyon baya da suke bata a dukkan matakan rayuwa, tana mai cewa su ne ginshiƙin nasararta.
Batuola ta roƙi Allah (SWT) Ya ƙara musu imani, ilimi, kunya da gaskiya, tare da sanya hijab ya zama abin alfahari da ɗaukaka a duniya da lahira.

Post a Comment