Makarantar Babul Ilmi Academy Ta Shirya Wa Dalibanta Da Suka Kammala Digiri Walimanta

 

Da yammacin ranar Lahadi, 19 ga watan Oktoba, 2025, ne aka gabatar da gagarumar walima Don taya daliban Makarantar Babul Ilmi Academy, Layin Tsamiya Hayin Dogo Samaru Zaria, Ta shirya wa Dalibanta walimar kammala karatun Degree daga wasu daga manyan makarantu da Jami'o'in kasar nan.  Dalibai Goma sha Hudu, da suka yi karatuka ta fannoni daban daban, ne aka yi ma Walimar. 

Daga cikin manyan bakin da suka Halarta akwai Professor Habib Dan Malam da Dr, Isah Waziri Gwantu, dukkansu  daga jami'ar Ahmadu Bello Zaria, Inda suka gabatar da jawabai tare yi masu nasihohi dangane da yadda za su ci gaba rayuwa bayan kammala karatun Digiri na farko, tare da karfafasu domin su ci gaba da karatu tare koyon sana'a domin dogaro da kai.  Jama'a da dama ne suka samu halartar walimar domin taya su murna da fatan Alkhairi.

Post a Comment

Previous Post Next Post