Mutane 244 suka mutu a Najeriya bayan kamuwa da cutar kwalara

Najeriya ta samu mutuwar mutane 244 sakamakon barkewar cutar kwalara tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na 2025, a cewar sabon rahoton  Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Rahoton, wanda aka buga a ranar Juma'a, ya nuna cewa ʙasar ta sami mutane 10,353 da ake kyautata sun kamu da cutar a cikin watanni tara.

A cikin kwanaki 28 da suka gabata kadai, Najeriya ta bayar da rahoton sabbin mutane 615 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 10, wanda hakan ke nuna raguwar wandada suka kamu da cutar da kusan kashi 1.6 cikin 100.

Rahoton ya kara da cewa, "Kwalara a Najeriya  inda mutane  kusan 10,353 suka kamu;aka kuma samu mutane 244 da suka mutu.

A fadin Afirka, rahoton ya nuna cewa ʙasashe da dama na ci gaba da fama da cutar ta kwalara, inda Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC), Angola, da Sudan ta Kudu suka sami mafi yawan adadi.

A DRCongo rahotanni na nuni cewa an samu mutane 56,696 da suka kamu da cutar da kuma 1,713 suka mutu, yayin da Angola ta samu mutane 29,347 da suka kamu, 809 suka mutu.

A Habasha, an samu mutane masu dauke da cutar 7,558 70 suka mutu,Ghana ,mutane 2,662 suka kamu da cutar,yayinda 14 suka mutu.Mozambik ta bada rahoton mutane 4,266 ne suka kamu da cutar,inda mutane35 suka mutu.

Post a Comment

Previous Post Next Post