Shaikh Ahmad Yashi Bauchi ya bayyana cewa, bayan an kashe ƴan uwa Musulmi a Zaria, Yarima Salman ya ce "Ba ma son abunda ya faru a Iran ne ya faru a Najeriya" Sun sakankance cewa matukar wannan mutum (Sayyid Zakzaky ) yana raye, lallai za a samu juyi a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa; wannan kisan da su Buhari suka aukar domin ganin bayan Sayyid Zakzaky (H), to lallai Sayyid ɗin ne ya yi nasara a kansu.
Yace; "Lokacin da suke shirin afka wa Malam Zakzaky (H), cewa musu aka yi idan har ba su kuskure ba a ranar 12 ga watan 12 da ƙarfe 12, to za su yi nasarar (Gamawa da Sayyid Zakzaky) amma gashi ba su yi nasara ba."
Wakilin ƴan uwa Musulmi na Da'irar Bauchi Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ne ya bayyana haka a ranar Talata 12-12-2023, a yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tunawa da waƙi'ar Buhari wanda ya gudana a garin Bauchi.
Daga wakilinmu

Post a Comment