'BABBAN ALAMI DA YA HADA DUKKANIN AL'UMMAR MUSULMI SHINE ANNABI (S)..'


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Yace;

“Babban alami da ya hada dukkannin al’ummar Musulmi shine Annabi (S), saboda babu wani wanda yake da wani ra’ayi daban dangane da Annabi (S). Yanzu da za a tambayi Nasara, za a ga suna da ra’ayoyi daban-daban dangane da Isa (AS), wasu za su ce shi Ubangiji ne, wasu za su ce Dan Ubangiji ne, wasu suce shi da Ubangiji ne suka hadu da ruhu mai tsarki suka zama Ubangiji, wasu kuma da har yanzu akwai su ‘yan kadan ne, suna cewa shi bawan Allah ne, dan sako ne.

“Amma in ka tambayi dukkanin Musulmi ko a ina ka same su a duniya, kace musu Muhammad (S) dan Allah ne ko kuwa shima Ubangiji ne? kowa zai ce Subhanallah! Ai kowannenmu ma kullum a sallarsa sai yace “Ashhadu anna Muhammadan Abduhu wa Rasuluhu.” Sai yace masa “Abd” kafin yace masa “Rasul”. Kowa na shaidawa da Manzon nan bawan Allah ne, kuma Manzon Allah ne. Kullum ana kiran Sallah da Iqama ace Annabi bawan Allah ne kuma ManzonSa ne. Ittifakan ba wanda zai ce maka shi Ubangiji ne.”

Cikin Jawabin Shaikh Zakzaky (H) ranar Maulud. Yayin ganawa da 'yan uwa. A ranar Laraba, 16 ga Rabi’ul Auwal, 1444 (14/10/2022).

Daga Bashir Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post