Kamar kowace shekara bana ma yan uwa Hurrasul Harakatil Islamiyya na Kudan Unit, yankin Zaria ta gabas sun gabatar da gagarumin Maulidin Shaikh Usman Bn Fodio kamar yadda jagora Syed Zakzaky (h) ya assasa masu duk shekara, bana ma taron ya gudana cikin nasara.
Taron dai da Harisawan Kudan Unit suka saba shiryawa duk shekara, tsawon shekaru kusan 12. Ya sami halartar dinbin al'ummar musulmi almajiran Syed Ibraheem Zakzaky (H) na yankin.
An haifi Sheikh Usman bin Fodio ne a rana irin ta yau ashirin da tara (29) ga watan safar.
Tunda farko dai sai da aka gabatar da muzaharar da ta hada yan fareti manya da yara maza da mata suka zagaya manyan titunan cikin garin Kudan da faretin ban girma ga Shaikh Usman Bn Fodio (T.R) daga bisani aka karkareta a fadar mai martaba sarkin Kudan.
A lokacin kammala taron cikin fili an gabatar da fareti da kareti wanda Harisawa suka gabatar. Daga karshe wakilin yan uwa na garin Bari, Malam Ahmad ya gabatar da jawabin rufewa wanda ya gabatar da gamsasshen jawabi kan tarihin rayuwar Shaikh Usman Bn Fodio, rayuwarsa, gwagwarmayarsa, da jihadinsa, sannan ya karkare jawabinsa da wasiyyar #DanFodio ta busharar zuwan Ibrahim da siffofinsa.

Post a Comment