Yadda aka gudanar da taron Makon Imam Husaini a garin Bomo


Daga Sukhainah Muhammad, Bashir Adam Muhammad, da Mardiyya Kabiru

TARON MAKON IMAM HUSSAIN (AS) RANA TA FARKO (1)

A ranar Asabar 16 ga watan muharram wanda yai daidai da 12 ga watan Yuli. Wanda Yan uwa almajiran sayyid Ibrahim Zakzaky (H). Dake garin Bomo suke gudanarwa. Wanda a wannan rana Babban bakon mai jawabin: Dr. Mika'il Ibrahim Tohu ne ya zama Babban Malami agun Wanda zaiyi Jawabi Akan maudu'insa Mai Taken.

WANE NE IMAM HUSSAIN (AS)

Taron ya fara da bude taron  da addua,  sai ziyarar Imam Husain (as). Shehin Malamin na Darikar Tijjaniya,  ya fara da kawo hadisan da Annabi  Muhammad (S.A.W.W)  ya bayyana taurari sun tabbata ne akan iyalen gidan Annabi Muhammad (SAWW) yake cewa duk Wanda yabi wa'innan iyalan annabin ya tabbata a hanya madaidaiciya. An ruwai to wata rana mala'ika jibril (As)  yazo gun manzon Allah (s) bayan mala'ika ya wuce, sai sahabbai suke cewa ya Muhammad Ka sanar damu wasiyyanka sai yake cewa Aliyu bin Abi Dalib  sai Hassan da Hussain sai 'yayan Hussain (As).  

Da zasu zo guda 9 sai Wani mutum yake cewa ya sunan su. Sai ya lissafa mashi tun daga Imam Ali har zuwa Imam mahadi (Ajf). Sheikh Ahmad Tijjani yana cewa wannan hasken iyalan Annabin ba wanda ya sameshi sai masoyin su. Wata rana Annabi yaje gidan sayyada Fatima  (As) Lokacin tana  zaune Imam Hassan na daman ta Imam Husain (As) na hagun ta sai Imam Ali (As). akwance yake cemata ya Fatima  ke da Imam Hassan da Imam Husain da Mai baccin can Muna tare agidan aljannah. A karshe yake cewa indai zaka iyayin mauludi Dan Wani Wanda kake so to abin da yafi kamata shine kayi akan iyalan gidan Annabi (As) da Taya manzon mu jaje aranan kinsan su (as). 

Yana cewa Shikanshi sunan shi Yana alamta Babu kaman shine al Hussain  (As). Rayuwan Imam Husain na tafene da tarihin da duniya Bata taba ganin irin Sa ba. Da zalincin da duniya Bata taba gani ba. Imam Hussaini  tun kafin  haihuwan shi. Aka fara mai kukan mutuwa sabida zalincin da zai riska. Daga cikin  jawabansa yace; wannan ayyukan da muke aika tawa a wannan duniyan wallahi ba irin na  Muhammadu rasululahi (s) mukeyi ba sallan mu, Hajjin mu, zakkan mu, duk ba irin Yanda Annabi (s) Yace muyi ba muke yi. Fitan  da Imam Husain (as).  Yayi ne shine yabamu daman Sanin abin da zamuyi a rayuwanmu. 

Da bai sadaukar da  ruwan Shiba yayi gwagwarmaya ba da bamu san wacce hanya ce madaidaiciya ba. Sannan malam. ya Kara da cewa wata rana Manzon Allah (SAWA). Yana cewa man ahabbani wa ahabba Huma wa Abu Huma wa umuhu to tabbas Muna tare acikin aljannan. Manzon Allah (SAWW) Yace man ahabba husaina fakad ahabbani wa man abgada hussaina fakad abgada ni. Yake cewa wannan zaman ba Yan shia bane kawai yakamata ace suke yi yan darikan Tijjani ya da Yan izala da duk masoyin manzon Allah (s) yadace ace Yana irin wannan munasaban.

12/07/2025.

TARON MAKON IMAM HUSSAIN (AS) RANA TA (2



A ranar Lahadi rana ta 2 Wanda yan uwa Almajiran Sayyed zakzaky (H) Na garin Bomo suke gabatarwa ayau Lahadi Wanda yayi dai dai   17 gawan muharram,  13 ga watan Yuli. Sheikh Auwal Alaba  Lagos ne ya zama Babban Bako Mai Jawabi Akan maudu'insa mai taken ‘MANUFAR FITOWAR IMAM HUSSAIN (A'S) ZUWA KUFA DAN JADDADA ADDININ KAKANSA’. An fara da bude taron da addu’a sai ziyaran Imam Husain (as). 

Dagan Shehin Malamin ya fara jawwbinsa Mai Albarka. Ya kawo Abubuwa masu mahimmanci akan Annabi Muhammad (SAWW) sannan yashiga cikin jawabinsa. Ya kawo lokacin wafatin manzon Allah da halin da sayyada Fatima (A's)  tashiga lokacin da Wani sahabi yashiga gidan ta ya hadata da kware ya karya mata awazan ta.  Kuma har izuwa lokacin da sukazo suka tafi da imam Ali domin yin Bai'ah har zuwa lokacin da taje gun su sukasa wani bawa yai mata duka. Har yazama sanadin wafatin ta alokacin da aka kaita fada sai take cewa shin ba nice Fatima ba yar manzon ku sai take cewa bokuji manzon Allah (s) Yace Allah na yarda da yar dana ba ?? 

Hakika Haske yazomaku daga manzon Allah (s) da littafin  Allah Yake cewa Imam Ali hakika gaske na agareka ne Kuma kaine littafin. Shi imam Hussain (as). Allah ya azir tashi da abinda Bai ma Wani halittaba, bayan su kakan shi shine shugaban mumunai, baban shi shine zakin Allah. Maman shi itace shugaban matan aljannan yayan shi shine  shugaban samarin aljannan. Imam Hussain (as). shine Annabi yagayama duk matansa cewa bana bukatan kukan wannan Wanda takai har inyana sallah yahau bayanshi yakan jira yasauka domin kar yar yai kuka. Akwai hadisin da yazo yake cewa wannan addinin tafara ne da Muhammad Amma tabba tuwan shi shine Hussain (as).  

Dalilin fitan Imam Husain (as) shine tun bayan kwana uku da wafatin manzon Allah (s) an canza komi shiyasa nauyin dawowa da Abubuwan da aka canza Yana wuyan Imam Husain (as). Imam Husain (A's) yaje  wajan Imam Hassan Yana kuka sai yake cewa ya Hussain Mai kakema kuka sai yake cewa inama zalincin da za amane kuka sai yake cewa; Ya Hussain aduniya Babu Wani yini irin yinin ka wanda mayaka dubu talatin zasu sauka akan ka. Kuma su wa'innan mayakan suna da awan suna bin tafarkin manzon Allah ne zasu diran maka.su farma yayan ka da sahabbanka, da matanka. 

Za su jasu amatsayin bayi Wanda duk Wani nau in Dabba zatai kuka da mutuwan ka. Imam Husain (A's) yafitane Dan ya gyara tsakanin al,umman kakan sa sannan yakasan ce cikin da awan mahai finshi ya karike da awan su. Wannan sadau karwan nashi shine ya Yantar da wannan da awan shi. Kadan daga cikin Jawabin shehin Malamin kenan.

MAKON IMAM HUSSAIN (AS) A RANA TA (3)

Yan'uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H)Na Garin Bomo Sunci Gaba Da Gabatar Da Zaman Makon Imam Hussain (AS) wanda Aka Fara Tin Ranar Asabar 12/7/2025. A ranar Litinin 14/7/2025 Zaman yacigaba daga inda aka tsaya. Matasa Sun Gabatar Wakoki Na Juyayi Da Tinawa Da Kisan Gillar Da Sojoji Bisa Umurnin Yazid Dan Maawiya(L) Sukaima Iyalan Gidan Manzon Allah(S). 

Bayan Kammalawa ne sai Babban Malamin Daya Samu Halarta Dr. Aliyu Ardido Zariya Inda Yake Cewa_ Bayan Gabatar da Addua da yayi, sai yatafi tsai Tsaye zuwa ga jawabinsa. Akan maudu'insa Mai Taken: Ma'anar Nasarar Addinin Musulunci, da Luggan Makamai. Shehin Malamin Yayi Jawabi Mai tsawon gaske  tare da kawo nasarorin da Addinin Musulunci yasamu. Inda ya nufi Karbala da irin kirare kiraren mutanen Kufa ga Imam Husain (as) Akan yazo ya koyar dasu Addinin kakansa (s). Sannan yafadi irin kalan Matsalolin da Imam Husain ya fuskanta da masa'ib kala kala daga rundunar Yazidu Dan mu'awiyyah. Malamin yacigaba da cewa, da za,a girmama masu tsoron Allah gaba daya to da zai zama iyalan Gidan Annabi ne(S)sune shuwagabannin masu tsoron Allah. 

Indai kaso Ahlulbait (As). to duk masifar duniya za'a turemaka, ashe idan munga musibu na bibiyanmu to munki son sune ahlulbait(AS). Babu daya daga cikin wanda zai zo yace yana sonmu face an bashi guba ko an kasheshi. Duk wanda yasan Ubangiji to ta hanyar Iyalan Gidan Manzon Allah(S) ya sanshi. Sannan Yace kin Iyalan Gidan Manzon Allah (S) kafircine. Ya Karkare jawabinsa da cewa Allah ya kashemu da son iyalan Gidan Manzon Allah (S). Sannan Wakilin Yan'uwa Na Garin Bomo Yayi Tahliki Kadan Akan Jawabin Da Babban Malamin ya yi. Babban Malami Shi ne Ya Samu Damar Rufe Taro da Addua.


14/72025

Labbaika ya Husain 

Labbaika ya Husain 

Labbaika ya Husain

MAKON IMAM HUSSAIN (AS) A RANA TA (4)


Yan'uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Ya'qub Alzakzaky(H)Suna Cigaba Da Gudanar Da Makon Iman Hussain(h)Agarin Bomo Dake Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya. Matasa Sun Gudanar Da Wakokin Juyayi Na Tunawa Da Kisan Gillar Da Sojoji Bisa Umurnin Yazid Bn Mu'awiyya(L) sukayiwa Imam Husain (as). Daga Nan shehi yafara jawabinsa. Malam Nazifi Ibrahim Samaru shine yayi Jawabi akan: MAUDU'I:MAKOMAN AZZALIMAI BAYAN WAKI'AR KARBALA. Daga Cikin Jawabin Malamin Na Darikar Tijjaniya. 

Yana Cewa; Fatima bintu Muhammad ta dakko Imam Hassan(AS) da Hussain(AS) takai su gun Manzon Allah(S)sai yake cewa wakeso yaga haiba irin ta Annabi Ibrahim(AS)to yayi duba zuwa ga Iman Hussain(AS) Duk Mai yadda da shi'a ko darika ko Sunnah indai zaibi halayya irin ta Imam Hussain(AS)to zai kasance dan shi'a ne. Duk wanda ya taba iyalan gidan Annabi(S) komin girman shi komin rawanin shi komin hidiman da yayima Manzon Allah(S)to dan wuta ne. 

Wani mutum daga cikin wa inda suka dokko kan imam Hussain(AS)yaje yana da wafi nana rokon tuba sosai yana rokon Allah ya gafarta mashi sai wani mutum yake cemai wannan rokon da kake ya isa Allah ya amsa sai yake cewa Ina da yakini ni Allah bai yafeman ba sai yake cemai kai ko wani zununi ka aikata sai yake cewa inadaya daga cikin mutanen 70 Wanda suka dakko kan imam Hussain(AS)atasa dan haka duk falalan da Allah ya tanadarwa wanda ya ziyarci dakin ka'aba  bazai man ba. Ya karkare jawabin nasa cewa duk mutumin da ke shi'a ko darika ko wata darikan kar kabari asameka baka da soyayyan iyalan gidan Manzon Allah (S). A karshe Mal. Muhammad Barau Samaru yai tahaliki akan jawabin da ya yi. Sai rufe taron Da Addua

Makon Iman Hussain(AS)
Labbaika Ya Hussain(AS)
Labbaika Ya Alzakzaky (H)
Haihatamin Nan Zillah
Ashura1446/2025

MAKON IMAM HUSSAIN (AS) A RANA TA (5)


Yan'uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) Na Garin Bomo Suna Cigaba Da Gudanar Da Makon Imam Hussain(AS)A Fudiyya Bomo Dake Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya. Bayan Bude Taro Da Addua An Kamsasa Wajen Da Ayoyin Alqur'ani Mai Girma. Babban Bakonmu Daya Samu Halartan Wajen Shine Sheikh Aliyu Tirmizi wato wakilin 'Yan uwa na Kaduna. 

Inda Ya Gabatar da maudu'insa Mai Taken: GUDUMMUWAR DA ABULFADL YA BAMA IMAM HUSSAIN (AS). Daga Cikin Jawabin Nasa Yana Cewa; DALILIN SAMUWAR ABULFADL ABBAS(AS). Iman Ali Bin Abi Talib(AS)yasa anemo masa mata wanda danginta suke da karfi domin ya samarwa Imam Hussain(AS) wanda zai taimaka masa a filin karbala sai aka samar masa da Ummu Banin wacce take a kabilar Banu Kilab shine ta haifo masa Abulfadl da Usman da wannan ne yasa ya zama mai karfi saboda jarumtar dangin mahaifiyarsa da mahaifinsa, kuma shine dalilin da yasa Imam Aliy ya wakilta abulfadl amatsayin wanda zai taimaki Imam Hussain (AS).

 
 JARUMTARSA 

Abulfadl shine na'abocin tutar Imam Hussain (AS) afilin karbala. Mutane dubu hudu suka tasoma Abulfadl Abbas(AS) lokacin da ya rike tutar Imam Hussain(AS) domin yaje debo ruwa suna kewaye dashine amma yana yin kurawa saida suka watse dukkansu saboda jarumtarsa kuma daman suffar jikinsa na jarumtane.  Azzalumai basujin dadin kawoma Imam farmaki ba har saida sukaji labarin Abulfadl Abbas (AS) yayi shahada, sannan sukaji cewa zasu iya farma Imam Hussain (AS) kai tsaye. Alokacin da ya zamana 'ya'yan  Imam Hussain (AS) da matan sa sunajin kishin ruwa yaroki Imam Hussain (AS) ya bashi daman domin yaje ya debo masu ruwa lokacin da yaje yana masu wa'azi yana cewa shin banine dan Ali Bin Abu Talib(AS) ba dan Ummu Banin yar kabilan Abu kilab sai suke cewa mun Sani.  

Amma bazamu baka daman kawuce ba har sai kayi wulaya ga yazidu Nan take ya rataya jaka mutane da suka tinkareshi mutun dubu hudu amma ahakan ya budasu ya je wajan diban ruwan bayan ya cika jakan nashi yadiba zaisha sai yatuna Imam Hussain (AS) da sukhaina (as) basu sha ba sai yatashi yana tafiya wani mutun ya boye abayan dabino yasaremai hannun dama sai yamayar hannun hagunsa yamayar bakin shi yana cewa wannan hannune kuka sare. 

Amma baku isa ku sare man Imanina ba sai suka harbeshi a ido ya fadi sai yabude murya yace ya Hussain bayan Iman(AS) yazo sai Iman Hussain (AS) yaga idonsa  daya dake da lafiya na hawaye sai yake cewa mekakema kuka sai yace  ina kukane saboda zan tafi na barka ba mataimaki nakiraka kazo kai wa zai zogareka alokacin da kake neman taimako. Sai yace bara nakai ka runfa sai yace aa banaso Sayyida Sukaina(AS) taganni bayan namata alkawarin zan kawo mata ruwa gashi ban Samu na cika mata alkawari ba. kuma ya Imam idan ka kaini rumfa zuciyar sauran zata raunana. Abulfadl Abbas (AS)shine garkuwan Imam Hussain (AS). Daga Karshe Ya Karkare Da Fadin Abulfadl Abbas (AS)yana nuna mana Tsantsar wulaya ne, da sadaukarwa. Daga Karshe An Rufe Taron Da Addua

Makon Iman Hussain(AS)
Assalamu Alal Hussain
Labbaika Ya Hussain (AS)
Labbaika Ya Alzakzaky(H)
Haihatamin Nan Zillah 🏿
1446/2025

MAKON IMAM HUSSAIN (AS) A RANA TA (6)


Yan'uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Ya'qoub Alzakzaky(H)Na Garin Bomo Sunaci Gaba Da Gudanar Da Makon Imam Hussain(AS) A Fudiyya Bomo Dake Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya. Bayan Bude Taro Da Addua An Kamsasa Wajen Da Karanta Wasu Ayoyi Daga Cikin Alqur'ani Mai Girma. Babban Bakonmu Daya Samu Halartan Wajen Shine Malam Buhari Wurn maudu'insa Mai Taken: HUDUBAR DA SAYYIDA ZAINABUL KUBRA(AS)TAYI A FADAR YAZIDU(L.A). Daga Cikin Jawabin Nasa Yana Cewa; Menene Asalin Sunan Zainab? Zainab wata itaciya ce mai kyau, kamshi, tana fitar da ganyaye masu kyau, shiyasa aka samata suna Zainab.

NASABARTA

Mahaifinta Shine Amirulmu'umimin (as) Mahaifiyarta Sayyida Zahra(AS)Yayanta Imam Hassan Da Iman Hussain(AS)Kakanta Shine Shugaban Halittun Duniya Da Lahira Muhammad Dan Abdallah(SAWW). Lokacin Da Aka Haifeta . Ubangiji Ya Aiko Da Sunan Asamata. Sannan Tanada Lakabi Har Guda Hamsin Da Uku Daga Ciki Akwai. Dalilin Da Yasa Ake Kiranta Ummul Masa'ib, Saboda Taga Masibobi Da Dama Ciki Harda Wafatin Manzon Allah(S). A gaban Idonta Aka Duki Mahaifiyarta sayyada Zahra (as), Aka Karya Kashin  Awazarta Tana Gani Aka Shahadantar Da Mahaifinta.  Tana Gani Aka Zubama Dan'uwanta Hassan(AS)Guba Jikinsa Saida Ya Dawo Shudi Sannan Agaban Idonta Akayi Waki'ar Karbala. Makocin Sayyida Zainab(AS)Yana Cewa Tunda Yake Bai Taba Ganin Fuskarta Ba Kuma Bai Taba Jin Sautinta ba, Har Saida Akai Waki'ar Karbala. Sayyida Zainab Mace ce Mai Tsananin Fasaha Acikin Maganarta Kuma Bata Da Tsoro. Idan Kacire Abulfadl Abbas(AS) To Babu Kamar Sayyida Zainab(AS) Afilin Karbala. A dare Na Goma Sayyada Zainab (as) Tana Kula Da Imam Ali Zainul Abidin(AS) Sai Taji Imam Hussain(AS) Na Raira Wani Waka Wanda Ke Nuna Yanda Za'a Kashe Shi. Jin Haka Sai Ta Tashi Taje Gun Imam Hussain(AS) Tana Kuka Take Cewa Wannan Na Nuna Kasheka Za'ayi Kenan ? Sai Ta Fara Marin Kanta Tarta Suma Sai Imam Hussain(AS) Ya Yayyafa Mata Ruwa. Lokacin da Imam Hussain(AS) Yake Fadin Halmin Nasirun Yansirna Sai Imam Ali Zainul Abidin(AS) Ya Tashi Zai Tafi Sai Imam Hussain(AS) Ya Ce Ya Zainab Kirikeshi Domin Shi Zai zamo Wasiyyina. Alokacin Da Akasama Tantinsu Wuta Ana Dukansu Sayyada Zainab Taje Tana Karesu Har Aka Yagamata Hijabi, wa musibata. Lokacin Da Aka Shigo Kufa Mutane Nata Kuka Sai Imam Ali Zainul Abidin(AS)  ta haramta.    Anje Fada Sayyada Zainab Tana Gefe Sai Sauran Matan Sukaje Tagefenta Sai Yazid(LA) Yake Cewa Wacece Wancan Taje Gefe Ta Zaune ? Yana Magana  Har Sau 3 Sai Matan Dake Gefenta Suke Cewa Itace Zainab Bin Aliyu Bn Abu Dalib(AS). Sai Yake Cewa Yaki kagani  Yanzu A farko Bata Bashi Amsa ba Sai Daga Baya Har Tai Jawabin Datayi Mai Jan Hankali Wanda Har Saida Yayi Danasanin  barinta. Tayi magana wannan Yasa  yayi Ninyar Kasheta Sai Akecemai Baa Kashe Mace. Antafi Dasu Izuwa Fadan Yazidu Wasu Akafa Wasu Akan Rakumi Ba Siddi Imam Aliyu Zainul Abidin(AS) Kuma Yana Acikin Sarka Da Mari Har Zuwa Sham 

HUDUBAR SAYYIDA ZAINAB A FADAR YAZID (L.A)


Ta Fara Da Godiya Ga Allah Da Tsinema Fajirai Da Masu Karyata Ayoyin Allah. Tana Cewa Ya Yazidu Halan Dan Katakuramune Yasa Mukawayi Gari Ana Koramu Kaman Bayi. Kai Girma Tabbata Agareka? Kana Ganin Wulakacin Dai Mana Kafimu Kusanci Ga Alah Kana Hura Hancinka Kazo kana Bugun Kirjinka Sabida Farin Ciki Ayayin Dakaga Duniya Kaman Takoma Naka? Kaman Al'ummah Sun Koma Gareka Sannan Mulki To,  Ka Saurara Kaji  Yakai Dan dan Sakakku Kana Ganin Kayi Adalci Kasa Mata Da 'Ya'yan Iyalan Gidan Annabi(S) Makiya Na yawo Dasu Daga Gari Zuwa Gari Mashaya Duk Abubuwan Da kayi Bai Ishekaba. Har Kana Cewa Wani Inda Yan'uwan ka Dasuka Zama Matattu Da Sunanan Zasu Yaba Maka?? Alhali Lokacin Da Kake Hakan Rauni Har Yanzu Yana Zuba Sannan Har Yanzu Muna Cikin Wahala Bayan Kazubar da Jinin Taurarin Kasa. Kasani Nan Gaba Kadan Bada Dadewa ba Zakaje Mazauninka, Sai ka Gwama ce Uwarka Bata Haifeka Ba. Ya Allah Ka Kwatan Mana  hakkin Mu Ga Wa'inda Suka Zubar  Da Jinanan Zuriyar Annabi(AS) Ka Keta Alfarmansa  Kada Kai Tsanmanin Wanda Aka Kashe Atafarkin Allah Matattu ne  Aa Rayayyune Awajen Ubangiji Ahaka Taita Masu Huduba. Daga karshe Kuma Ya Karkare Jawabin Nasa Da Cewa.  Da badan Sayyida Zainab Kubra(AS)Da Ba'asan Al'amarin Ashura Gaba Daya ba. Daga karshe shehin Malamin ya fure Taron da Addua.

Makon Iman Hussain(AS)
Assalamu Alal Hussain
Labbaika Ya Hussain(AS)
Labbaika Ya Alzakzaky(h)
Haihatamin Nan Zillah
1446/2025

MAKON IMAN HUSSAIN A MADARASATUL FUDIYYA BOMO  LIL- ULUMUDINIYYA WALI IHYA-ISHA'AIRIL HUSSAINIYA

MAKON IMAM HUSAINI RANA TA KARSHE




Yan'uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Ya'qoub Alzakzaky(H)Na Garin Bomo Sunyi Khatma Dinsu Na Makon Iman Hussain(AS)A Fudiyya Bomo Dake Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya. Bayan Bude Taro Da Addu'a An Kamsasa Wajen Da Karatun Alqur'ani Daga Cikin Alqur'ani Mai Girma . Matasa Sun Gabatar Da Zikiri Na Tunawa Da Kisan Gillar Da Sojoji Bisa Umurnin Yazid Bn Mu'awiyya(L.A)Sukaiwa Iyalan Gidan Manzon Allah(S). 

Acikin Rana Da Kishirwa Wanda Ya Kara Shajja'a Rijalai. An Karanta Ziyarar Aba Abdallahil Hussain(AS). Sannan Yara Sun Gabatar Da Display Mai Rasa Zuciya Da Saka Kuka Duk Awajen Makon Iman Hussain(AS). Baban Bakonmu Daya Samu Halartan Wajen Shine Sheikh Abdulhamid Bello Zariya Wanda Malam Auwal Hanwa Ya Samu Gabatar Dashi MAUDU'I_SHAHIDAN WAKI'AR KARBALA. Daga Cikin Jawabin Nasa Yana Cewa. An haifi Imam Hussain(AS)awatan sha'aban manzon Allah(S)yayi farin ciki sosai lokacin da aka kawo masa Iman Hussain(AS)sai kuma akaga ya fashe da kuka sai aka tambayeshi mai yasa shi kuka sai yace Mala'ika Jibril (AS)yace mashi wasu daga cikin al'ummarsa sune zasu kashe Aba Abdallah(AS) Sannan ya kara da magana akan yadda su Iman Hussain(AS)suka baro garin makkah har zuwa inda sukaita yada zango har zuwa lokacin da makiya Allah sukai masu kawanya Rundunar Iman Hussain(AS) basu wuce 430 cikinsu  harda mata da kananan yara rundunar Iman Hussain sunsan cewa duk wanda ya fita bazai dawo ba dan haka duka sun shirya su bada ransu domin fansan ran Aba Abdallah(AS). 

Iyalan gidan Manzon Allah(S)sun fuskanci abubuwa da dama ciki harda hanasu ruwa da akai na tsawon kwanaki uku ciki harda kananana yara. Baa tabayin sahabbai irin sahabban Iman Hussain(AS)inda suka nuna sudin yan halasne sunsan cewa zaa kashe su amma suka zabi su tsaya su bada ransu domin fansan Aba Abdallahil Hussain(AS). Iman Ali Zainul Abidin(AS)ya bukaci cewa duk abinda ya nema zaa bashi sai akace mashi eh sai yace yanaso ya assasa zaman makokin yanaso ya sanarma duniya ainihin abinda akai masu. Ya karkare jawabin nasa da cewa al'amarin ashura babban al'amarine kuma da badon Iman Hussain(AS)ya bada rayuwarsa da yanzu Addininma babu saboda shine ya fanshi Addinin Allah daga wajen munafukai. Dan'uwa Malam Abduhamid Dahiru ya kara karfafa ma yan'uwa gwiwa akan ku dake mu dake kuma muyi aikin saboda Allah. Sannan Sha'irul Hussain Auwal K Mashi yazo yayi majalisi awajen 


Makon Iman Hussain(AS)
Assalamu Alal Hussain(AS)
Labbaika Ya Hussain(AS)
Labbaika Ya Alzakzaky(H)
Haihatamin Nan Zillah 🏻
Makon Iman Hussain1446/2025


Post a Comment

Previous Post Next Post