Da Safiyar ranar Asabar 27/07/2025 ƴan'uwa Musulmai Almajiran Sayyid Ibrahim yaqub Al-Zakzaky (H) na Sassan garuruwa maban-banta ne suka ziyarci makwancin Sarkin Musulmai Shehu Attahiru Mborni Almajirin SHEHU USMAN DAN FODIYO , shi da sauran ƴan uwansa Shahidan (27 july) wanda turawan mulkin mallaka suka yiwa Dalar gawawwaki a shekarar 1903, yau she ƙara 122 kenan a garin Mborni dake Bajoga jahar Gombe.
Turawan mulkin mallaka (turawan yamma), Sunyi wa Al'majiran Shehu Usman Dan Fodiyo kisan gilla haɗi da yin dala na gawawwaki a Nbormi Sannan Suka yiwa Al-Qur'ani fitsari Suka Ƙona, daga nanne Suka ɗora Mana Consitution Wanda har wala yau Shi yake iko damu a wannan ƙasa tamu Nigeria, ba Al-Qur'ani ba. Ziyaran ta gudana ne yau Asabar a Makwancin Shahidan, inda aka gabatar da karanta Ziyaran Ashura da Sauran Addu'o'i maban-banta, sannan Aka gabatar da Zikira (Azah) na Waƙen abubuwan da Ya faru dasu Shuhada, a Wannan muhalli wasu daga cikin ma halarta na kuka haɗi da Bugan ƙirji!, bayan kammalawa aikai addu'ar tashi, kana aka ɗora da Muzzahara zuwa cikin garin Bajoga.
Gefe guda kuma Muna ƙara sanar da Sauren Musulmai cewa, ana gabatar da gagarumin program a wannan Muhallin a watan December ƙarshen kowacce shekara, Kasantuwar watan 7 yana zuwa lokacin damuna ne, kar aɓatawa manoma, amfanin gona kuma taron yana samun halarta mutane Dubbai, hakan yasa Jagora Sayyid Ibrahim Zakzaky (H), yayi umarni da a dinga yin program din a watan December Duk Shekara Saboda Kar a shiga haƙƙin manoman yankin wajen.
Post a Comment