An gudanar da jana'izar hamshaƙin ɗankasuwar nan na Najeriya, Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Annabi (S.A.W) da ke birnin Madina.
Jana'izar ta gudana ne bayan sallar magariba, inda kuma aka binne gawarsa a maƙabarta Baƙiyya mai tarihi a birnin na Madina. Mutane da dama ne daga Najeriya suka halarci jana'izar - wadda aka jinkirta tun da farko sakamakon wasu dalilai na ciƙa ƙa'ida. Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ta halarci jana'izar, tare da tawaga mai ƙarfi da ta ƙunshi manyan jagororin jihar. A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaida wa BBC. Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya shaida wa BBC. Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha'awarsa cewa "Allah ka kashe ni a wannan gari" a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya. Tuni dai tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na ƙasar Saudiyya domin halartar jana'izar Alhaji Aminu Ɗantata ta isa ƙasar.
Tawagar gwamnatin tarayyar ƙarƙashin jagorancin ministan tsaron ƙasar, tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) da ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata da dai sauran su.
Akwai kuma manyan malamai a cikin tawagar da suka haɗa da sheikh Aminu Daurawa da Dr Bashir Aliyu Umar da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad. Shi ma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa birnin na Madina tare da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II da gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, da tsohon gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa'ad Birnin Kudu, da sauran manyan jami'an gwamnati da dattawan jihar Kano.
Marigayi Aminu Dantata, wanda ya shahara wajen kasuwanci da sadaka da hidimar jama'a, ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa. "Mutuwarsa ta bar giɓi a harkokin tattalin arziki da walwalar al'umma, tare da kammala wani babi mai muhimmanci a tarihin Najeriya," in ji sanarwar gwamnatin jihar Kano.
Wane ne marigayi Aminu Ɗantata?
An haifi Alhaji Aminu Ɗantata, a shekarar 1931. Shi ne na 15 a wajen mahaifinsa Alhassan Ɗantata, wanda ya haifi 'ya'ya 17 jimilla. Mutane kan kira shi Aminu Dogo saboda tsawon da yake da shi. Ya yi karatun firamare a Dala Primary School da ke birnin Kano, da kuma na Islamiyya kafin ya halarci sakandaren da mahaifinsa ya gina.
Iyalin Ɗantata kan fara koyon neman kuɗi tun suna da ƙananan shekaru. "Mu a dinginmu yaro kan fara neman kuɗi tun yana da shekara biyar ko shida ko bakwai," kamar yadda ya bayyana cikin wata hira ta musamman da kafar talabijin ta Trust TV a watan Mayun 2024. "Mahaifinmu kan ce mana 'kun ga yadda mutane ke kawo gyaɗa a raƙuma da jakuna, to ya kamata ku ma ku san yadda za ku fara neman kuɗi. Lokacin da muke zuwa makaranta kuma, mahaifinmu kan yi amfani da lokutan hutu yana koya mana yadda za mu yi kasuwanci."
Ya fara nisa a harkokin kasuwanci tun yana shekara 17 lokacin da ya maye gurbin yayansa Ahmadu Ɗantata a matsayin shugaban tashar kasuwancin da mahaifinsu Alhassan ya kafa da ke garin Bichi a jihar Kano. Kafin rasuwar mahaifin nasu a 1955, Alhaji Alhassan ya kafa kamfani mai suna Alhassan Ɗantata and Sons. Daga baya Aminu ya koma jihar Sokoto, inda ya shugabanci reshen kamfanin a can. Ya zama mataimakin shugaban kamfanin a 1958, yayin da Ahmadu ke shugaba, sai kuma ya maye gurbin yayan nasa a matsayin shugaba bayan rasuwarsa a 1960.
Ya kafa ko kuma an kafa kamfanoni da dama tare da shi, ciki har da na man fetur mai suna Express Petroleum & Gas Company Ltd, da bankin Jaiz Bank. Wani kamfaninsa na gine-gine ne ya gina kwalejin horar da tuƙin jirgin sama da ke Zariya a shekarar 1960. Yana cikin majalisar ƙoli ta farko da ta kafa bankin kasuwanci na gwamnatin Najeriya Nigerian Industrial Development Bank (NIDB), wanda a yanzu ya koma Bank of Industry (BOI). Zuwa yanzu babu wasu alƙaluma da ke bayyana ɗimbin dukiyar da ya mallaka.
Post a Comment