Dandalin Matasan Harakar Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Sayyed Ibrahim Zakzaky (H), na garin Gwandu dake Imam Ali Arridha (AS) Zone (Sokoto) sun gabatar da aikin gayya ga wata Marainiya wacce ta rasa Mahaifi da kuma Mahaifiya. Iyayen rasu suna da ƴaƴan biyu, kuma dukkansu mata ne, kuma duk sun yi aure, ɗayar ce aurenta ya mutu, anan take zaune , sai ya zama gidan nasu ginin ƙasa ne, a kwana a tashi wasu ɓangarorin gidan suka faɗi, har ta kai bazai yiyu ta kwana a gidan ba sai, ta je cikin gidan maƙwabta.
Ta kai koken ta zuwa ga Yan uwanta da kuma Maƙwabtanta domin a taimaka mata, amman abin bai samuba, wannan ya sa al'amarin ya kai Matasa su ka ji ƙorafinta, nan take suka share mata hawaye. Wannan aikin dai an share tsawon lokaci ana yinsa. An soma gabatar aikin ne ranar Lahadi 25/05/2025 har zuwa Alhamis 19/06/2025, inda aka ware ranar Lahadi da Litinin na kowane mako domin gudanar da wannan aikin har zuwa wannan lokacin da aka kammalashi.
Youth From Media Team

Post a Comment