A ranar Laraba 18/6/2025 Yan'uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Ya'qoub Alzakzay(H) na garin Bomo suka gabatar da bikin murna na zagayowar ranar da Manzon Allah(S) ya nasabta kuma ya shelenta Imam Aliy bin Abu Talib(A S). A matsayin kalifansa kuma wasiyinsa a doron kasa. Bayan bude taro da Addua an gabatar karatun Alqurani mai girma. Sai Malam Aliyu Dalhatu Bomo, Shima ya Tofa albarkacin Bakinsa Akan wanene Imam Ali (as). Da nuna godiya ga Allah bisa Ni'imar Fahimtar damu falalar wannan Rana ta Edil Ghadeer. Sai Na'ibin Bomo Malam Nuhu Haliru yayi takaitaccen bayani kuma masu kayatarwa akan yaumul ghadir inda yakema Allah godiya akan ni'iman da yayima muka fahinci wasiyancin da Manzon Allah(S) yayi.
Sannan ya kara da magana akan nasarorin da jamhuriyar musulunci ta Iran take samu yanzu. Malam Auwal Hanwa Shine Ya Zama Babban Malami Mai Jawabi awajen gagarumin taron. Inda Shehin malamin Yafara da Kawo darajoji da matsayi na Imam Ali (as). Inda yace Tun ranar da aka haifi iman Ali(AS) Manzon Allah yake shelenta cewa wannan shine wazirina.
Manzon Allah(S) ya kasance yana tara mutanensa yana fadamasu cewa shi dan aiken Allah ne ga bayinsa kuma Manzon karshe a doron kasa. Imam Ali (as). ya kasance yana taimakon Manzon Allah (as). tun farkon bayyanar da musulunci da Manzon Allah (saww) yayi ga al'ummar zamaninsa. Allah(SWT) Ya Sanya Iman Aliy(AS) ga manzon Allah (s) kamar yadda Haruna yake a wajen Musa (as) saidai shi Aliy ba Annabi bane Tun daga farkon Annabawa har zuwa Annabin karshe Annabi Muhammad(S) kowa yana da nasa wasiyyin da zai gajeshi a doran kasa bayan yayi wafati. Sannan ya kare da bayani akan yadda ranar idil ghadir ya kasance a hajjin bankwana da Manzon Allah (saww) yayi kafin yabar duniya.
Daga cikin abinda ya faru a hajjin bankwana; Manzon Allah (saww) ya kasance yana tausayawa mutanen da zasuji sakon ammah bazasu yarda ba. Inda mala'ika yazo har sau uku akan ya isar da sakon da akeso ya isar Inda ya kawo ayar da ta sauka cikin suratul ma'ida aya ta 67 akan lallai Manzon Allah ya isar da sakon nan. Bi yarage ga Al ummah. Kadan daga cikin jawabinsa kenan. Anfara lafiya Kuma antashi lafiya.

Post a Comment