An samu ƙaruwar tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya a ƙasar ta gabashin Afrika tun bayan da rikici ya ɓarke tsakanin shugaban ƙasar Salva Kiir da mataimakinsa na farko Riek Machar. Tsare Machar da aka yi a watan Maris a babban birnin ƙasar Juba na daga cikin abubuwan da suka ƙara ta’azzara rikicin, har ma ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a ƙasar suka bayar da rahoton kai hari a asibitoci da kuma yadda ake farmakar fararen hula.
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu ta ce a tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin shekarar 2025, an kashe fararen hula 739, baya ga 679 da suka jikkata, yayin da aka yi garkuwa da 149 wasu 40 kuma suka fuskanci cin zarafi. Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce idan aka kwatanta da watanni ukun baya, an samu ƙaruwar kashi 110 a kashe-kashen da ake samu a ƙasar, adadin da ba’a taɓa gani ba tun shekarar 2020.
Ana alaƙanta mafi yawan kashe-kashen da aka samu da ƙungiyoyin sa kai, kodayake Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗora alhakin kashi 15 na kashe-kashen da ke faruwa kan bangaren gwamnati da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai. Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta sha yin gargaɗi kan rincaɓewar rikici a ƙasar, wadda har yanzu ke ƙoƙarin farfaɗowa daga yaƙin shekaru biyar tsakanin mabiya Kiir da Machar wanda aka kawo ƙarshen shi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu su ka yi a shekarar 2018.

Post a Comment