Cikin wata sanarwar bidiyo, Kakakin rundunar sojin Mali Souleymane Dembele ya ce, ƴan ta’adda da ya kira makiya sun yi babbar asara a duka cibiyoyin tsaro da suka kai wa harin, tare da nuna gawarwakin mayakan da suka mutu da makamansu da babura da motoci.
Tun da farko ƙungiyar JNIM mai alaka da al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai hare-hare barikokin sojin Mali, inda ta yi ikirarin ƙarbe iko barikoki uku da kuma wuraren sojoji da dama.
Dakarun sojin ƙasar sun ce an kai hare-haren ne a garuruwa bakwai na yankin tsakiya da yammacin ƙasar da ke yammacin Afirka.
Ƙasar Mali ƙarƙashin mulkin soji tun a shekarar 2020, ta shafe fiye da shekaru goma tana yaƙi da ƙungiyoyin ta'addanci masu alaka da ISIS da kuma al-Qaeda, yayin da take fama da dogon tarihi na tawayen da Abzinawa ke jagoranta a arewacin ƙasar.

Post a Comment