An Fara Zaman Juyayin Ashura A Fadin Tarayyar Nijeriya Na Wannan Shekarar 1447

A ranar 1 ga watan Muharram ta sabuwar shekarar 1447 aka shiga rana ta farko da fara zaman juyayin Ashura domin tunawa da kisan gillar da aka yiwa jikan Manzon Allah (SAWW) a filin falalin Karbala wato Imam Husaini (A.S) da Iyalansa da Sahabbansa bisa Jagorancin Umar bn Sa'ad da Umurnin Sarki Yazidu 'Dan Mu'awiyyah.

Taron wanda almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke gabatarwa a duk fadin 'kasarnan a duk shekara, a bana ma ba su yi 'kasa a guiwa ba inda suka shirya irin wadannan taro a dukkanin jihohin arewacin Nijeriya 19 ciki harda birnin Tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce kazalika an gudanar da taron a manyan birane da kauyaku fiye da 600 wanda suka hada da; Kaduna, Kano, Zariya, Katsina, Gusau, Saminaka, Yola, Bauchi, Potiskum, Dutsenma, Sakkwato, Abuja, Suleja, Funtuwa, Dabai, Malumfashi, Talatan Mafara, Jos, da sauran Jihohi da 'kananan garuruwa.

A lokacin taron, ana tunatar da mahalarta taron bayani dangane da wannan wa'ki'a ta ashura da irin yadda aka zalunci iyalan gidan Manzon Allah (SAWW). Da kuma kawo ruwayoyi daban-daban dangane da waki'ar Ashura a litattafan Musulunci domin daukar darasi daga rayuwar Imam Husaini da Sahabbansa na yadda ya dake akan tafarkin Kakansa Manzo (S).  A kowanne gari, taron na samun halartar dimbin 'yan uwa Maza da mata daga sassa daban-daban.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post