A ranar Asabar ne 'yan’uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na majalisin Bomo suka saka tutar Labbaika ya Hussain (as), a muhallin Fudiyyah Bomo. Sannan wakilin 'yan Uwa Na Bomo Malam Murtala Yusuf ya jagoranci zaman wannan rana. Ya fara da takaitaccen abin da ya faru a irin wannan ranar ta 2 Ga Muharram na isowar Imam Hussain (AS) da sahabbansa farfajiyar Karbala.
Post a Comment