Nijeriya: Mutane 600 da suka ɓace a ambaliyar Mokwa ba sa raye – ‘Yan Majalisa


 A wani ƙudiri na haɗin gwiwa da suka gabatar a yayin zaman majalisar wakilan ƙasar a wannan Laraba, Joshua Audu Gana daga Neja da Saba Ahmed Umaru daga Kwara sun koka akan irin ɓarnar da ambaliyar ta haddasa a Mokwa da wasu sassan ƙaramar hukumar Edu ta jihar Kwara.

A cewar ƴan majalisar, ambaliyar, wadda ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa a ranar 28 da 29, ta ta’azzara ne sakamakon rugujewar tsohuwar gadar jirgin ƙasa ta Mokwa, lamarin da ya sa ruwa ya mamaye mahimman yankunan Mokwa, ciki har da cibiyoyin kasuwanci kamar Tiffin Maza da Anguwan Hausawa.

Sun shaida wa majalisar cewa mutane 500 ne aka tabbata sun mutu, kana 600 suka ɓace, kuma har yanzu ba a gano su ba, lamarin da ya sa aka ɗauka ba sa raye, duba da irin girman iftila’in.

Sun ce ambaliyar ta lalata gidaje 4,000 gabaɗaya, ta kuma jikkata mutane 200, kana ta mamaye filayen gona masu yawa, tare da wargaje mahimman ababen more rayuwa, lamarin da ya jefa dubban mutane cikin halin neman gudummawar jinƙai.

‘Yan majalisar sun bayyana damuwa akan yadda lafiyar waɗanda suka tsallake rijiya da baya ke cikin haɗari, su na mai nuni da barazanar kamuwa da cutar kwalara da zazzaɓin typhoid, sakamakon gurɓacewar ruwa, da kuma yanayi na rashin tsafta a sansanonin da aka ajiye wadanda suka rasa muhallanssu.

Post a Comment

Previous Post Next Post