Wata sanarwa da Atiku Abubakar din ya fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan al’amuran yaɗa labarai Paul Ibe, ta ce, ɗa ga shugaban na Najeriya, wato Sheyi Tinubu wanda ke kokarin nemarwa mahaifinsa magoya baya ko ta halin ƙaƙa, na kokarin amfani da kujerar mahaifinsa wajen sanya shakku a zukatan jama'ar ƙasar. Atiku Abubakar ya bayyana cewa, wannan tsari da Sheyi Tinubu ya runguma, shakka babu, ba zai haifar da ɗa mai idanu ba.
Sanarwar ta ce, zargin da shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS, wato Atiku Isah ya yi, kan yunƙurin yin garkuwa da shi, bisa umarnin Sheyi Tinubu abin damuwa ne sosai. Wannan zargi da ake yiwa ɗan shugaban na Najeriya ya haifar da fargaba a zuƙatan ‘yan ƙasa da dama, la’akari da irin girman kujerar mahaifinsa, in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma yi watsi da zargin da ake yiwa tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, na haɗa kai da shugaban na NANS, Kwamred Isah wajen cimma wasu manufofi na siyasa, tare da shiryawa gwamnati mai ci bita da ƙulli.
Post a Comment