Al'ummar Masarautar Gitata, Ƙaramar Hukumar Karu, Jihar Nasarawa sun ziyarci Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), a gidansa da ke Abuja, da yammacin yau Lahadi.
A yayin ziyarar Jagora ya fayyace wasu batutuwa kan zamantakewar al'ummu daban-daban, sannan ya yaba da masu ziyarar. Inda aka tattauna batutuwan da ke damun al'ummar ƙasar nan, musamman ma Arewacin ƙasar da ke fama da matsalolin da aka jefa yankin karfi da yaji.
A nasu bangaren, shugaban tawagar, Mr. Yakubu wayas, Sarkin Ninzo, Gitata Chiefdom, Karu LGC, ya nuna godiyarsa ga Allah da ya samu kawowa Jagora wannan ziyarar, inda ya gabatar da jaje kan abubuwan da suka faru. A cewarsa; Tun Mallam ya na tsare na ce wa yan uwa in Allah ya yarda Mallam zai fito, ba abinda zai faru da shi, tunda bai zalunci kowa ba.
Ya ƙara da cewa; Bisa abinda muke karantawa a littafanmu (Bible), mun tabbatar Annabawa sun sha wuya. Kuma abinda muke gani ya nuna shi ma Mallam ya na kan hanya irin ta Annabawa.
@SzakzakyOffice
@SZakzakysGallery
#FreePalestine
#PrayForPalestine
#OurMartyrsOurHeroes
20/04/2025

Post a Comment