OPEC ta ce za ta Kara yawan man da take fitarwa



Ƙungiyar Opec da ƙawayenta sun amince da ƙara yawan man fetur da suke fitarwa zuwa kasuwar duniya a watan Yuni, duk kuwa da karyewar farashin man a kasuwar duniya sakamakon raguwar buƙatarsa.

 Farashin man fetur ya yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba cikin watan Afrilu, inda aka sayar da gangar mai kan dala 60, bayan da Opec da ƙawayenta suka ayyana ƙara yawan man da suke haƙowa a watan Mayu.

 Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato majiyar OPEC na bayyana cewa Saudiyya na buƙatar a ladabtar da mambobin ƙungiyar iraƙi da Kazakhstan saboda saɓa ƙa'idar yawan da da ƙungiyar ta amince su fitar. A baya-bayan nan ne Dnald Trump ya yi kira ga ƙungiyar OPEC ta ƙara yawan man da take fitarwa. A cikin wannan wata na Mayu ake sa ran Shugaba Trump zai ziyarci Saudiyya.

Post a Comment

Previous Post Next Post