Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC ta bayyana cewa an karkatar da kashi 71 cikin 100 na Naira biliyan 100 da gwamnati ta fitar domin bai wa daliban jami’o’i lamunin karatu ƙarƙashin shirin NELFUND.
Hukumar ta gano wannan badaƙala ne bayan gudanar da zuzzurfan bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da gwamnatin tarayyar ƙasar ta fitar ta hanyar shirin bayar da lamunin karatu ta NELFUND.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Demola Bakare ya fitar ya ce duk da cewa gwamnati ta fitar da Naira biliyan 100 don bai wa dalibai bashi, amma Naira biliyan 28.8 ne kaɗai ya isa zuwa ga dalibai a jami’o’in da ke sassan Najeriya.
Wannan bincike ya samo asali ne bayan da kafafen yaɗa labarai suka wallafa labarin da ke zargin jami’o’i 51 na zaftare kuɗaɗen lamunin da ake bai wa dalibai da Naira 3,500 zuwa 30,000.
Hakan ne yasa hukumar ICPC ta gayyaci shugaban shirin na NELFUND domin ya bayar da bahasi kan yadda suka tafiyar da kuɗin.
Binciken ya ce asusun NELFUND ya samu kuɗaɗen shiga da suka kai Naira miliyan 203.8 ya zuwa 19 ga watan Maris na 2024,Naira biliyan 10 daga asusun haɗaka na gwamnatin tarayya, sai Naira biliyan 50 daga hukumar EFCC, da kuma Naira biliyan 71.9 har sau biyu dukkaninsu daga asusun tallafawa manyan makarantu na TETFUND.
To sai dai duk da irin tarin kuɗaɗen, iya Naira biliyan 44.2 ne aka fitar zuwa ga manyan makarantun a sassan ƙasar, kodayake ICPC ta tabbatar da cewa an aikata kura-kurai da dama a shirin lamunin, wanda ya sanya za ta faɗaɗa bincike zuwa manyan makarantun da kuma ɗalibai.

Post a Comment