Kisan gillar da wasu ƴanbindiga suka yi wa babban limamin Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Alƙali Salihu Suleiman, da ƴaƴasa uku ya harzuƙa al'umma. Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana lamarin a matsayin "wani mummunan matsayi" da matsalar garkuwa da mutane ta kai a Najeriya.
Cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar a Najeriya Isa Sanusi ya ce limamin mai shekara 79 da ƴaƴansa uku sun shiga hannun ƴanbindiga ne a lokacin azumin watan Ramadana a watan Maris kuma sun kashe su ne duk da karɓar kuɗin fansa naira miliyan 11 cikin miliyan 20 da suka buƙata. Amnesty ta bayyana cewa waɗanda lamarin ya shafa sun fuskanci "matsananciyar azaba" a hannun ƴanbindigan.
"Baya ga dukan da aka dinga yi musu kullum, yanbindigan sun hana su abinci da ruwa na tsawon lokaci “Amnesty International na Allah wadai da wannan kisan gilla. Abu ne mai tayar da hankali yadda irin waɗannan laifuka ke ci gaba da faruwa ba tare da hukunta masu aikata su ba."
Post a Comment