Daga Mardiyya Kabiru
Wani abin burgewa da ban sha'awa da Yan uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky, na garin Mani dake jihar Katsina, sun zama zakaran gwajin dafi inda suka fito mazansu da matansu yaransu da manyansu inda suka biya Haqqin Shuhada dinsu baki daya na wannan shekarar.
Wakilin Muassasa na yanki wanda kuma shine ya wakilci shugabar Muassasa ta kasa, ya bayyana cewar da za a samu dukkan dairori da halqoqi baki daya su aiwartar da irin wannan hikimar da ba za a samu matsala ba a harkokin gudanarwar Muassasa. Itama shigaban gudanarwar Muassasa ta kasa, Hajiya Maryam Sani, ta nuna farin cikinta da irin wannan tsarin da dairar Mani ta dauka, inda ta shawarci sauran dairori da su yi kayi da su domin hakan zai taimaka sosai. Wani abin birgewa shine yadda aka biya kudaden gaba daya ta sabon tsarin anfani da na'urar biyan kudin da Muassasa ta fitar don saukakawa.
Post a Comment