Taron Maulidin Shahadar Shahid Ahmad, Hameed Da Mahmoud Ibraheem Zakzaky A Abuja.


Matasan da ke zaune a garin Mararaba, sun gudanar da taron tunawa da shahadar ‘ya’yan Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) guda uku, wato Shahid Ahmad Zakzaky, Shahid Hameed Zakzaky da Shahid  Mahmud Zakzaky tare da wasu mutane talatin da daya (31) wanda ya hada da dan uwa Kirista daya, marigayi Julius Anyanyan, wadanda suka yi muzaharar  Qudus a Najeriya.  

Ranar 26 ga Yuli, 2014 a Zaria, Jihar Kaduna, a zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan. An fara taron ne da “Majlisul Aza” (na makokin shahidan) sannan aka gabatar da mai jawabi, dan uwa Muzaffar Ali, wanda ya yi jawabi mai dacewa da maudu’in wannan rana dangane da shahadar Yaya Ahmad da ‘yan uwansa.  Taron ya samu halartar 'yan uwa da dama domin karrama jaruman Harkar Musulunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post