A ranar Asabar ne 15/3/2025, wanda ya yi daidai da 15 ga Ramadan, 'yan uwa almajiran sayyed zakzaky (H) na majalisin Bomo suka gabatar Da Maulidin imam Hassa AS. Taro ya fara da bude taron da addu'a Wanda
Mal. Murtala Yusuf ya gabatar. Sannan sai karatun alqur 'ani wanda Ibrahim Sa'eed y agabatar. Ittihadu Shu'ara sun nuna nasu murnar ta hanyar qamsasa muhallin da baitocin Imam Hassan Almujtafha (AS). Saikuma jawabin taro din daga bakin Mal Yusuf Tahir Bomo. Daga cikin jawabin da malamin ya gabatar shi ne yake cewa Allah ya ambaci Imam Hassan Almujtafha (AS) acikin alqur'ani aqalla wajaje guda hudu 4 daga cikin ayar Innama yuridullaha liyuziba ankumun rijisa ahlul baiti wayu dahhirakum taddira .
An ruwaito daga Sahabi Abubakar na ga Manzon Allah (AS) ya rungumo Imam Hassan (AS) yana cewa wannan yaran ku yi riko da shi babu mamaki wata rana ya zama shugaban ku dan haka ku yi riko da shi jarabawar da Imam Hassan ya fuskanta. Allah ya jarabe shi da mata wacce Mu’awiyyah yasayeta da kudi Wanda harya kaida ta sa masa guba a abinci Wanda wannan guban shi ya yi sanadiyyar Shahadarsa, da sahabbai wanda a idon sa suke nuna suna tare da shi a bayan idon shi kuma suna tare da Mu’awiyyah, wanda yake turo su domin su ji mai sirran Imam Hassan (as).
Hakkan yasa imam Hassan yanemi ma awiya domin suyi zaman sulhu saboda yaqe-yaqen da ake wannan dalilin Mu’awiyyarsa ya tunanin ko Imam Hassan (As) ya yi saranda ne haryasa yaje kasuwa yana cewa ni ban yake kuba domin tabbatuwan alkur ani ko domin tabbatar da addini nayine domin tabbatar dacewa ni shugaban kune Kuma dole kubini Kuma na warware alkawarina da imam Hassan (as) Kuma nabarranta da shi. Kadan daga cikin Jawabin malam Yusuf Bomo ke nan.
Daga Bashir Adam
15/3/2025
Post a Comment