A safiyar ranar Lahadi 30/03/2025 wanda yayi dai dai da daya ga watan shauwal 1446 ne, yan uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na garin Zaria suka gudanar da sallar idi karama a Zaria din, Sheikh Abdulhamid Bello ne ya jagoranci sallar.
Dubbun nan yan uwa ne tare da wasu daga cikin mutanan gari suka halarci sallar da aka gudanar a safiyar yau Lahadi din.
A cikin Jawabin sa a wajen Sheikh Abdulhamid Bello yayi kira ga yan uwa su sauke nauyin da ya hau kansu na zakkatul Fitir don kuwa azumin mutum bai tafiya kai tsaye idan bai bada zakkatul fidir ba, da yayi tsokaci don gane da waki'ar Qudus kuwa ya baiyana cewa zamu gabatar da sallar jana'izar yan uwanu da jami'an tsaron soji suka kashe a Abuja wurin jerin gwanon muzaharar kudus bayan mun kammala sallar idi din, haka muna kara gayama azzalumai idan sunyi don su tsorata mu ne to mu ba zamu tsorata ba don kuwa kisa bai hanamu yin addini bayan ya kammala ne aka rufe taron da addu'a duk da kuwa, sannan aka gabatar da Jana'izar Shahidan
©Zaria Media Forum
1 Shawwal 1446
Post a Comment