Harkar Musulunci a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky, ta gudanar da muzaharar Ƙudus ta duniya ta 2025 a sama da birane 30 a faɗin ƙasar.
Wannan muzahara ta shekara-shekara, wanda ake gudanarwa domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu da ake zalunta a koyaushe, ya samu gagarumar halarta a manyan birane da garuruwa kamar Abuja, Zariya, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Jigawa, Jos, Bauchi, Nasarawa, Legas, Enugu, Kogi, Talatan Mafara, Kauran Namoda, Neja, Gombe, Potiskum, Yola, Kontagora, Azare, Darazo, Danja, Jidawa, Mashi, Zuru, Illela, Jalingo, Batsari, Daura, Birnin Kebbi, Yawuri, Dukku, Saminaka, Kafanchan, Dutsin-Ma, da Hadejia, da sauransu.
A bana, an gudanar da wannan muzahar a ranar Juma'a 28 ga Ramadan 1446 (28 ga Maris, 2025), inda masu muzaharar suka jaddada goyon bayan Harkar Musulunci ga al’ummar Falasɗinu ba tare da gajiyawa ba.
Dubban ɗaruruwan masu muzaharar, wanda ya haɗa maza, mata, da matasa, sun yi tattaki cikin lumana suna rera taken kamar "’Yanci ga Falasɗinu" da "A kawo ƙarshen zaluncin Isra’ila." Masu muzaharar suna ɗauke da kwalaye da alluna masu saƙonni irin su "Dukanmu Falasɗinu ne" da kuma "A dakatar da kisan kare dangi a Gaza."
Ranar Ƙudus ta duniya, wacce jagoran juyin juya halin Musulunci, Imam Ayatollah Khomeini, ya ayyana a shekarar 1980, ta zama wata alama a duniya wajen fafutukar ’yancin Falasɗinu daga mamayar Isra’ila. Kazalika a Nijeriya kaɗai ba, ana kuma gudanar da irin wannan muzaharar a ƙasashe kamar Birtaniya, Amurka, Jamus, Kanada, Faransa, Ostiraliya, da kuma a Asiya ta yamma, Afirka, Latin Amurka, da sauran su.
Duk da yanayin muzaharar ta kasance cikin tsari da lumana a faɗin ƙasarnan, amma a birnin Tarayya Abuja jami’an sojojin Nijeriya (Guard Brigade) sun farmaki masu muzaharar, wanda ya haifar da hasarar rayuka.
Jami’an sojin sun buɗe wuta kan masu muzaharar a Bannex, inda suka kashe fiye da mutane 20 ya zuwa haɗa wannan rahoto, suka kuma jikkata wasu da dama, kuma suka kama fiye da mutum 20 ba bisa ƙa’ida ba.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an yi amfani da harsasai masu rai kan masu muzaharar da ba su da makamai, wanda hakan take haƙƙin ɗan Adam ne.
Dama kafin wannan muzaharori, ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya fitar da rahoton ƙarya, yana nuna cewa wannan gagarumar muzaharar barazana ce ga tsaro. Harkar Musulunci ta yi Allah wadai da wannan ƙarya, tana mai cewa an yi hakan ne domin hana wannan muzaharar wacce yake halal ce a ƙoƙarin kare muradun ƙasashen waje, musamman Amurka da Isra’ila.
Tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, Isra`ila ta ƙara tsananta hare-haren soja kan Gaza`, inda ta jefa fiye da bama-bamai 100,000, ta kashe akalla Falasɗinawa 50,000, tare da jikkata fiye da 90,000—galibinsu yara. Fiye da kaso 90% na gidaje a Gaza` an rushe su, tare da lalata wuraren ibada, makarantu, asibitoci, da kasuwanni.
Harkar Musulunci ta yi Allah wadai da wannan zalunci da ake yi wa al’ummar Falasɗinu raunana, tare da kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki cikin gaggawa kan kisan kare dangi da ake ci gaba da yi.
Haka kuma, Harkar Musulunci ta buƙaci a saki dukkannin waɗanda aka kama a Abuja nan take, tare da kira ga gwamnatin Nijeriya da ta riƙa mutunta ’yancin gudanar da taron lumana, kamar yadda kundin tsarin mulkinta da dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya suka tanada.
Muzaharar Ƙudus ta duniya tana nan a matsayin wata babbar alama ta yaƙi da zalunci a duniya, kuma Harkar Musulunci tana mai jaddada aniyarta na ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da al’ummar Falasɗinu komin runtsi.
Muna kira ga dukkan masu hankali da ƴan adamtaka da sanin ya kamata, ko mene ne kuwa addininsu ko ƙasarsu, da su ci gaba da bayyana goyon bayansu ga adalci tare da Allah-wadai da zalunci ko da wa za su saɓawa.
© Ammar Muhammad Rajab
Post a Comment